Mijina Bai Kwanta Da Ni Ba Tsawon Shekaru 2, Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Su

Mijina Bai Kwanta Da Ni Ba Tsawon Shekaru 2, Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Su

  • Ruqayya Mukhtar, matar aure mai shekaru 25 ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta, Naziru Hamza
  • Matar ta yi zargin cewa shekaru biyu kenan rabon mijinta ya kusanceta da sunan auratayya
  • Sai dai, Hamza ya karyata zargin nata inda ya ce yana iya bakin kokarinsa wajen biya mata bukatarta amma ita kullun sai ta nemi a tara da ita

Jihar Kaduna - Wata matar aure mai shekaru 25, Ruqayya Mukhtar ta fada ma wata kotun Shari'a da ke Rigasa, jihar Kaduna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, cewa mijinta bai kwanta da ita ba tsawon shekaru biyu.

Mai karar wacce ta nemi kotu ta raba aurenta da wani mai Naziru Hamza ta kuma koka cewa mijin nata na cin zarafi da mutuncinta, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Shi Ya Dauki Nauyin Karatuna": Bayan Shekaru 3 a Turai, Budurwa Ta Dawo Najeriya Don Samun Saurayinta Bakanike, Bidiyon Ya Yadu

Mata na karar mijinta saboda rashin bata hakkinta
Mijina Bai Kwanta Da Ni Ba Tsawon Shekaru 2, Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Su
Asali: UGC

Ina iya bakina da matata amma ita kullun sai dai a kusance ta, magidanci

Da yake kare kansa, wanda ake karar ya karyata zargin cewa yana iya bakin kokarinsa don biyawa matarsa bukatarta ta bangaren auratayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Tunda ina fita kullun don neman na abinci, Wasu lokutan ina dawowa gida da dare ne kuma a gajiye amma matata bata fahimta, a kodayaushe tana so na kusance ta.
"Na kan amsa mata sau da yawa sannan wasu lokutan na kan roketa ta yi hakuri har zuwa washe gari kuma bana dukanta."

Wane mataki alƙalin kotun ya fara ɗauka?

Alkalin, Anas Khalifa, ya tambayi mai karar ko tana da shaidu kuma ta amsa da eh.

Ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 5 ga watan Satumba don mai karar ta gabatar da shaidunta.

Kara karanta wannan

Yadda Likitoci Suka Gano Tana Mai Rai A Kwakwalwar Wata Mata

Wani mutum ya saki matansa uku a rana daya, ya fadi dalili

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutumin kasar Uganda, Mutiatya, ya saki matansa uku a rana daya, inda suka tafi suka barsa da yara bakwai.

Afrimax ta yi hira da mutumin mai shekaru 55, wanda ya ziyarci kasashe 14, sannan ta bayyana dalilin da yasa ya rabu da matansa.

Mutiatya ya ce ya saki matansa saboda munanan halayensu. Ya tuna yadda abubuwa ke tafiya daidai a bayan har zuwa lokacin da ya rasa aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel