Fadar Shugaban Kasa Tayi Umarni a Dakatar da Binciken Kudi a Ma’aikatar Fetur

Fadar Shugaban Kasa Tayi Umarni a Dakatar da Binciken Kudi a Ma’aikatar Fetur

  • Fadar shugaban kasa ta fitar da takarda da ta dakatar da aikin kwamitin da aka kafawa hukumar NUPRC
  • Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya sa hannu a takardar nan mai lamba SH/COS/24/A/28 kwanaki
  • Femi Gbajabiamila ya sanar da ma’aikatar man fetur cewa an kai maganar binciken NUPRC gaban AGF

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Fadar shugaban kasa ta umarci Ma’aikatar harkokin man fetur ta kasa ta dakatar da binciken da ta ta ke shirin yi a hukumar NUPRC.

A cewar Premium Times, umarnin ya fito a wata takarda mai lamba SH/COS/24/A/28 da ta fito daga Aso Rock Vill a ranar 1 ga watan Agusta 2023.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya sa hannu, yake cewa ma’aikatar ta ajiye batun kafa wani kwamiti.

Shugaban kasa
Femi Gbajabiamila a fadar shugaban kasa Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

Umarnin da Femi Gbajabiamila ya bada

Kara karanta wannan

Aiki ya fara: Daga zuwa, Ganduje ya yi sabbin nade-nade a kwamitin NWC na APC

"An kai batun kafa kwamitinku da zai binciki asusun NUPRC zuwa ga Ministan shari’a, HAGF domin ya duba a matakinsa a dokar kasa da tsarin aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda haka ana umartar kwamitinku ya dakatar da ayyukansu zuwa lokacin da HAGF zai gama aiki."

- Femi Gbajabiamila

Rahoton ya ce an fitar da wannan umarni ne a lokacin da rigima tayi kamari tsakanin shugabannin hukumar NUPRC da ma’aikatan karkashinsu.

An taso Gbenga Komolafe a gaba

Kungiyar PENGASSAN ta zargi shugaban hukumar tarayyar da toshe hakkokin ma’aikata, su ka bukaci a tsige Gbenga Komolafe daga kan kujerarsa.

PENGASSAN ta na ikirarin ana zaftare fanshon ma’aikata, babu isassun kayan aiki, an ki biyan ma’aikata albashi da alawus tare da rashin kiwon lafiya.

...NUPRC ta musanya zargi

Hukumar kasar ta karyata wadannan zargi, ta kuma ce tuhumarta da ake yi da bada gudumuwar N10bn a lokacin yakin neman zabe ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Babbar Sarki Ya Najeriya Ya Tunatar da Tinubu, Ya Faɗi Hanya 1 da Za a Karya Farashin Man Fetur

Wani ma’aikacin hukumar ya shaida mana cewa tun da aka kawo Gbenga Komolafe bayan an rattaba hannu a kan dokar PIA, abubuwa su ka birkice.

A cewar wannan jami’i da aka boye sunansa, shugaban na NUPRC ya yi alwashin durkusar da hukumar, har abin ya yi sanadiyyar shirya zanga-zanga.

Shari'ar Godwin Emefiele

Ku na da labari Godwin Emefiele ya na so ya sawakewa kotu shan wahala a shari’ar da ake yi da shi na satar N6.9bn a lokacin da yake gwamnaa CBN.

Shari'ar ta je gaban kuliya tun tuni, amma har yau Alkali Husseini Baba Yusuf bai fara sauraron shari’ar ba, ana tunanin za sasanta ne ta bayan-fage.

Asali: Legit.ng

Online view pixel