Matashi Ya Kwanta Har Kasa Ya Na Rokon Tinubu Da Cewa Yunwa Za Ta Hallaka 'Yan Najeriya, Bidiyon Ya Yadu

Matashi Ya Kwanta Har Kasa Ya Na Rokon Tinubu Da Cewa Yunwa Za Ta Hallaka 'Yan Najeriya, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi ya kwanta har kasa ya na rokon Shugaba Bola Tinubu cikin Yarbanci da ya yi wa 'yan Najeriya rai don fitar da su a wannan hali
  • Wata mai ta'ammali da manhajar Twitter, Judith Akatugba ta wallafa faifan bidiyon a shafinta inda ta fassara bayanin zuwa harshen Turanci
  • Wannan na zuwa ne bayan 'yan kasar sun fita hayyacinsu saboda wasu matakai da Shugaba Bola Tinubu ke dauka da su ka shafi talakawa

'Yan Najeriya na cikin kunci da yunwa tun bayan cire tallafin mai wanda ya kara hauhawan farashin kayayyaki a kasuwannin kasar da dama.

Mutane na ta korafe-korafe a kan irin matakan da Shugaba Bola Tinubu ke dauka masu tsauri, Legit.ng ta tattaro.

Matashi ya je har kasa ya na rokon Shugaba Tinubu ya kawo dauki a kasar
Yadda Wani Matashi Ya Kwanta Har Kasa Ya Na Rokon Tinubu Kan Halin Da Ake Ciki. Hoto: @OfficialABAT and @judithakatugba.
Asali: Twitter

Wani roko matashin ya yi wa Tinubu?

Ganin irin halin kunci da ake ciki, an shawarci Shugaba Tinubu da ya kawo wa 'yan Najeriya dauki kada yunwa ta kashe su.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Sauki Ya Zo Yayin Da Tinubu Ya Shirya Siyar Da Litar Gas Naira 250 Madadin Fetur, Ya Tura Bukata Ga 'Yan Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, an gano wani matashi ya kwanta har kasa ya na rokon Tinubu a cikin harshen Yarbanci.

An fassara kalmominsa na Yarbanci zuwa Turanci kamar haka:

"Baba Tinubu ka yi hakuri, ba mu da wata harkar kasuwa yanzu.
"Mun zabe ka, ka ji tausayinmu ka da ka sa mu yi dana sanin zabanka.
"Dan Allah ka yi hakuri, yunwa za ta hallaka mu."

'Yan Najeriya na cikin kunci tun bayan da Shugaba Tinubu ya cire tallafin mai a watan Mayu.

Wacece ta wallafa bidiyon da ake rokon Tinubu?

Wata mai ta'ammali da manhajar Twitter, Judith Akatugba ta wallafa faifan bidiyo a shafinta inda ta fassara shi zuwa harshen Turanci.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Tinubu Ya Mayar Da 'Yan Najeriya Fursunonin Yaki, COSEY

Kara karanta wannan

Tallafin N5bn: Tinubu Na Amfani Da Kudin Don Tilasta Karin Kudin Mai, Kungiya Ta Soki Tsarin Shugaban

A wani labarin, Gamayyar Shugabannin Matasan Kudu maso Gabas, COSEY ta bayyana cewa Shugaba Tinubu na son tilasta 'yan kasar amincewa da karin kudin mai karfi da yaji.

Kungiyar ta ce shugaban ya fito da tsarin tallafin kudade ne don rufe bakin mutane tare da kakaba musu tsadar mai din a dole.

Ta ce Tinubu ya dauki 'yan Najeriya marasa wayo inda ya mayar da su kamar fursunonin yaki inda ba sa iya cewa komai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel