Tinubu Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Shirya, Zai Siyar Da Iskar Gas Naira 250 Ko Wace Lita

Tinubu Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Shirya, Zai Siyar Da Iskar Gas Naira 250 Ko Wace Lita

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sanar da siyar da iskar gas a kan Naira 250 ko wace lita
  • Gwamnatin Tarayya ta bukaci mutane su mayar da ababan hawansu zuwa masu amfani da iskar gas
  • Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke siyan litar man fetur daga Naira 580 har zuwa Naira 640 a fadin kasar

FCT, Abuja - Shugba Bola Tinubu ya sanar da siyar da iskar gas a kan Naira 250 a kan ko wace lita daya.

Hadimin shugaban, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce sun shirya kawo sauki a kasar.

Tinubu ya sanar da siyar da litar iskar gas Naira 250
Tinubu Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Shirya Amfani Da Iskar Gas Madadin Fetur. Hoto: Indiantimes.
Asali: Facebook

Meye Tinubu ya ce kan amfanin Gas?

Iskar gas din ita za ta maye gurbin bakin mai da kuma man fetur da mutane ke amfani da su a harkokinsu na yau da kullum, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ana Rigima a Kan Kujerar Minista 1 Da Ta Ragewa Bola Tinubu Ya Nada a Gwamnati

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ngelale ya ce Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da cewa an yi amfani da iskar gas din a madadin man fetur don samun sauki ga al'umma.

Ya kara da cewa tsarin wanda shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila ke jagoranta zai samar da motoci dubu 11,500 masu amfani da iskar gas don kawo sauki a sufuri.

Wane tsari Tinubu ke yi kan Iskar gas?

Ya ce:

"Wannan tsari ya na da matukar muhimmanci ga Tinubu saboda rage amfani da fetur kuma 'yan Najeriya na shan wahala kan hauhawan farashin kayayyaki.
"Shi ne dalilin da yasa Tinubu ya kawo wannan tsari don rage wahalhalu a bangaren sufuri ga 'yan Najeriya."

Ya ce gwamnati za ta yi kokarin inganta tsarin samar da shi don karya farashin litar man fetur.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

"Kada Ka Bari Mu Yi Dana Sani": Matashi Ya Kwanta Har Kasa Ya Na Rokon Tinubu, Bidiyon Ya Yadu

"A nan tsammanin ku biya Naira 250 a ko wace lita na iskar gas, hakan zai karya farashin mai da ake siya a kan Naira 620 ko wace lita daya."

Tinubu Zai Mayar Da Ababawan Hawa Zama Masu Amfani Da Gas

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya za ta sauya wa mutane ababan hawa daga masu amfani da fetur zuwa iskar gas.

Hukumar Koyar Da Fasahar Sufuri a Najeriya, NITT ita ta yi wannan alkawari yayin da ake fama da tsadar man fetur a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel