Hankali Ya Tashi Yayin da Zanga-Zanga Ta Barke a Kano Kan Shirin ECOWAS Na Yakar Sojojin Nijar

Hankali Ya Tashi Yayin da Zanga-Zanga Ta Barke a Kano Kan Shirin ECOWAS Na Yakar Sojojin Nijar

  • Rahoton da muke samu daga jihar Kano ya bayyana cewa, an yi zanga-zangar nuna adawa da aniyar ECOWAS
  • Wannan yanayin na zuwa ne bayan da kungiyar ta bayyana daukar matakin soja ka wadanda suka yi juyin mulki a Nijar
  • An hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, lamarin da ya jawo cece-kuce a nahiyar Afrika da ma duniya

Jihar Kano - Wasu masu zanga-zangar sun karade tituna a jihar Kano domin nuna adawa da amfani da karfin soja da ake shirin yi don kawo karshen juyin mulkin Nijar.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta umurci dakarun sojinta na hadin gwiwa daga kasashe daban-daban da su kasance cikin shirin ko ta kwana don kai farmaki.

A ranar Asabar ne masu zanga-zangar suka fara nuna fushinsu da rashin jin dadinsu da shirin mamaye jamhuriyar Nijar da sojojin ke shirin yi nan gaba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Yadda aka yi zanga-zanga a Kano
An yi zanga-zangar nuna adawa da ECOWAS a Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yayin da suke tafiya cikin zulumi da nuna alhini, suna tafe rera wakar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“’Yan Nijar ’yan’uwanmu ne, ’yan Nijar danginmu ne.”

Yadda 'yan Najeriya suka ki yakar Nijar

A tun farko, 'yan Najeriya da dama sun bayyana rashin amincewarsu da yadda shugaban ECOWAS kuma shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya yunkuri bi da sojin Nijar.

Sun bayyana cewa, kasar Najeriya da Nijar duk daya ne, don haka yakar kasar daidai yake da yunkurin raba alakar da ke tsakani, rahoton Vanguard.

Wannan ne ma yasa majalisar dattawa a kasar ta bayyana cewa, bata tare da Tinubu a wannan matsaya ko kadan.

Hakazalika, ta ce ba za ta amince a tura sojin Najeriya wajen yakar wadanda suka yi juyin mulki a jamhuriyar ta Nijar ba.

Malaman Izala sun tafi sulhunta Nijar da ECOWAS

A wani labarin, fitattun malaman addinin Musulunci karkashin jagorancin shugaban kungiyar Jama’a tul Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa Sheikh Bala Lau, sun dira jamhuriyar Nijar a wani mataki na neman hanyar da za ta sa a sasanta lamarin da ya faru na juyin mulki.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Mazauna Nijar Sun Tura Muhimmin Sako Ga Tinubu, Sun Bayyana Matsayarsu

A hotunan da Legit.ng Hausa ta gani a shafin Twitter na kafar Zagazola Makama, an ga lokacin da malaman suka sauka a Nijar.

An gano malaman a filin jirgin sama, inda suka samu tarba daga jami’an sojin jamhuriyar ta Nijar da ke makwabataka da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.