Juyin Mulkin Nijar: Manyan Matakan ECOWAS 4 Da Suka Janyo Barazana Ga Rayuwar Bazoum

Juyin Mulkin Nijar: Manyan Matakan ECOWAS 4 Da Suka Janyo Barazana Ga Rayuwar Bazoum

Labari ya gama bazuwa cewa, sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar sun ƙuduri aniyar halaka hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

Hakan na zuwa ne bayan tsauraran matakan da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS ), ke ci gaba da ɗauka kan sojojin.

Kamfanin dillancin labaran AP ya yi rahoto cewa, wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka ya bayyana cewa, sojojin na Nijar sun yi barazanar kashe Bazoum idan ECOWAS ta tura sojoji kasar da zummar dawo da mulkin dimokuradiyya.

Sojojin Nijar sun sha alwashin halaka Bazoum
Matakan ECOWAS 4 da ke neman jefa rayuwar Bazoum cikin haɗari. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

ECOWAS ta bai wa sojojin wa'adin kwanaki bakwai

Biyo bayan juyin mulkin da sojojin na Nijar suka yi, ƙasashen ECOWAS da ke maƙwabtaka da jamhuriyar Nijar, sun yi Allah wadai da lamarin tare da bai wa sojojin kwanaki bakwai su maida mulki.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Jigon PDP Ya Faɗawa ECOWAS Muhimman Abubuwa 9 Da Ya Kamata Su Sani a Kan Sojojin Nijar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi biris da umarnin na ECOWAS, wanda hakan ya janyo wani taro na musamman da ƙungiyar ta yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Akwai wasu matakai guda huɗu masu tsauri da ƙungiyar ta ECOWAS ta ɗauka tun bayan juyin mulkin, waɗanda ake ganin sun fusata sojojin na Nijar. Matakan su ne:

1. Aika saƙon gargaɗi ga ƙasashen da ke goyon bayan sojojin Nijar

Kungiyar ECOWAS ta aikawa ƙasashen da ke goyon bayan sojojin juyin mulkin na jamhuriyar Nijar gargaɗi mai zafi dangane da abinda suka yi.

Ƙasashen da ECOWAS ta aikawa saƙon gargaɗin sun haɗa da Mali, Burkina Faso, Guinea, Mali da Guinea Bissau.

2. Neman haɗin kan AU da UN

Mataki na gaba mai tsauri da ake ganin ya fusata sojojin Nijar shi ne, neman goyon bayan Tarayyar Afrika (AU), da Majalisar ɗinkin Duniya (UN).

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Muhimman Abubuwa 12 Da Suka Faru Tun Lokacin Da Sojoji Suka Kifar Da Gwamnatin Bazoum

Idan AU da UN suka goyi bayan ECOWAS, ta hanyar marawa matakan da ta ɗauka baya, hakan zai iya janyowa sojojin na Nijar matsin lamba daga 'yan ƙasa, saboda da ƙuncin rayuwar da za su shiga.

3. Tabbatar da matakan da aka ɗauka a baya

A zama na biyu na musamman da shugabannin ECOWAS suka yi, sun yanke shawarar tabbatar da matakan da suka ɗauka kan Nijar da ƙwawayenta a baya.

Daga cikin matakan akwai rufe iyakoki, sanya takunkumin tafiye-tafiye da kuma riƙe kadarorin mutanen da ake tunanin suna taimakawa masu juyin mulkin.

4. Bai wa sojojin ECOWAS umarnin zama cikin ko ta kwana

Mataki na baya-bayan nan mafi tsauri da ECOWAS ta ɗauka, shi ne na bai wa sojojinta umarnin ɗaura ɗamarar yaƙi da sojojin juyin mulkin Nijar.

Wannan mataki ya ƙara tabbatar da matsayar ECOWAS ta farko, kan cewa za ta iya yin amfani da ƙarfin soji idan matakan diflomasiyya ba su yi aiki ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito

Shehu Sani ya caccaki Tinubu da ECOWAS kan matakin soji

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan caccakar da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi wa Tinubu da ƙungiyar ECOWAS.

Shehu Sani ya gargaɗi Shugaba Tinubu da kuma ƙungiyar ECOWAS, kan kar su yi kuskuren janyowa Najeriya yaƙi saboda matakin da suke shirin ɗauka kan jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel