Shugabannin Kungiyar Izala Sun Dira Nijar Domin Neman Sulhu a Batun Juyin Mulkin Soja

Shugabannin Kungiyar Izala Sun Dira Nijar Domin Neman Sulhu a Batun Juyin Mulkin Soja

  • Yanzu muke samun labarin yadda shugabannin Izala suka dira Yamai domin tabbatar da an samu mafita ga abin da ke faruwa a Nijar
  • An hambarar da mulkin dimokradiyya a Nijar, lamarin da ya jawo cece-kuce da bacin rai ga kungiyar ECOWAS
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da ba da shawarin amfani da teburin sulhu wajen tabbatar da an zauna lafiya a kasar

Yamai, Nijar - Fitattun malaman addinin Musulunci karkashin jagorancin shugaban kungiyar Jama’a tul Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa Sheikh Bala Lau, sun dira jamhuriyar Nijar a wani mataki na neman hanyar da za ta sa a sasanta lamarin da ya faru na juyin mulki.

A hotunan da Legit.ng Hausa ta gani a shafin Twitter na kafar Zagazola Makama, an ga lokacin da malaman suka sauka a Nijar.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara ce: Naja’atu Ta Tona Dalilin Shugaba Tinubu Na Tsokano ‘Yaki’ Da Nijar

An gano malaman a filin jirgin sama, inda suka samu tarba daga jami’an sojin jamhuriyar ta Nijar da ke makwabataka da Najeriya.

Malaman Izala a Nijar don sulhunta ECOWAS da sojoji
Lokacin da malaman suka dira jamhuriyar Nijar | Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Halin da ake ciki a Nijar

Tun bayan da sojojin Nijar suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, jamhriyar ta shiga wani yanayi na takunkumi daga kasashen duniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana ta kiraye-kiraye ga sojin Nijar da su mayar wa Bazoum mulkinsa cikin gaggawa ko kuma a dauki mataki a kansu.

Daga ciki, kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa, za ta dauki matakin soji kan Nijar idan mulkin bai koma ga Bazoum ba cikin kankanin lokaci.

Ku zauna cikin shiri, ECOWAS ga soji

A bangare guda, ECOWAS ta umarci sojojinta da su kwana da shirin tunkarar sojin Nijar don tabbatar da kwace mulkin.

Sai dai, a tun farko kungiyoyi da yawa, ciki har da na addini sun yi Allah-wadai da yunkurin daukar matakin soji.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Bayan kira ga sulhu, wannan ne yasa kungiyar Izala a yau ta yi tattaki zuwa Nijar don tabbatar da an samu mafita ga abin ke faruwa.

Zanga-zangar Kanawa

A bangare guda, wasu masu zanga-zangar sun karade tituna a jihar Kano domin nuna adawa da amfani da karfin soja da ake shirin yi don kawo karshen juyin mulkin Nijar.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta umurci dakarun sojinta na hadin gwiwa daga kasashe daban-daban da su kasance cikin shirin ko ta kwana don kai farmaki.

A ranar Asabar ne masu zanga-zangar suka fara nuna fushinsu da rashin jin dadinsu da shirin mamaye jamhuriyar Nijar da sojojin ke shirin yi nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel