Kyakkyawan Likita Ya Tashi Kan Yan Mata Yayin da Ya Saki Zafafan Hotunansa a Wajen Aiki, Sun Zauce

Kyakkyawan Likita Ya Tashi Kan Yan Mata Yayin da Ya Saki Zafafan Hotunansa a Wajen Aiki, Sun Zauce

  • Tsantsar kyawun wani likita ya sa shi daukar hankalin mutane da dama a dandalin soshiyal midiya
  • Hadadden likitan ya wallafa hotunansa a wajen aiki kuma ya tashi kan yan mata da dama
  • Yan mata da dama sun tambayi ina ne asibitinsa yake yayin da suka dungi kiransa da sunaye masu dadi wanda ke nuna suna sonsa

Wani likita mai suna Dr Jae, ya dauki hankalin yan mata da dama a soshiyal midiya saboda tsantsar kyawun da Allah ya yi masa.

Lamarin ya fara ne lokacin da Dr Jae ya saki zafafan hotunansa a bakin aiki kan TikTok da taken "Kowa na da rawan ganin da zai taka wannan shine nawa."

Kyakkyawan likita ya burge yan mata
Kyakkyawan Likita Ya Tashi Kan Yan Mata Yayin da Ya Saki Zafafan Hotunansa a Wajen Aiki, Sun Zauce Hoto: @dr_ehi_jae
Asali: TikTok

Wallafarsa na TikTok ya yadu, inda aka samu mutum fiye da miliyan 1.4 da suka kalla a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kara karanta wannan

“Ta Yi Kama Da Mutum”: Matashi Da Ya Gaza Samun Budurwa Ya Siya Mutum-Mutumi a Bidiyo

Sashinsa na sharhi ya cika da yan mata suna ta jinjinawa irin kyawun da yake da shi da kuma nuna yadda suke son mallakar shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu yan mata sun mata furta cewa za su so su dunga rashin lafiya a kodayaushe idan har za su gan shi a asibitin.

Yan mata sun zauce a kan hotunan likita

user9179334037621 ta ce:

"Kawai zan dunga rashin lafiya ne kullun sannan na dunga zuwa asibitinka."

nanamanga1 ta ce:

"Ba zan iya soyayya da duk kyawawan mazan nan ba faa ko Allah ma ya sani."

Mamzy ceesay ta ce:

"Ba na cikin yanayi mai kyau amma ganinka kawai sai na fara murmushi Allah ya albarkace ka."

Agyaa Collinsya ce:

"Yan mata da matan mutane a nan sashin sharhi..kuna da lafiya?"

Lady T ta ce:

Kara karanta wannan

“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Matashi Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiyar Rangwada Da Takalma Masu Tsini, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

"Abun da nake so kawai shine sunan asibitin. don Allah zuciyata na cikin radadi."

zikaluv ta ce:

"Kalli kyakkyawan mutum kungiyar masu so ku zo ku hadu a nan."

Kelly ya ce:

"Idan wannan ya taimakawa matata ta haihu matata na iya binsa fida daga nan."

Rashin budurwa ya sanya saurayi siyan mutum-mutumi

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani mutumi ya baje kolin mutum-mutuminsa a soshiyal midiya, yana mai cewa ya siye ta saboda ya gaza samun budurwa mutum.

A wani bidiyon TikTok, mutumin ya fito da mutum-mutuminsa mai tsawon mutum daga cikin kwali sannan ya dungi motsa jikinta da taimakon na'urar da ta zo da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel