Kyakkyawar Santaleliyar Budurwa Ta Ba da Mamaki, an Ganta Rike da Sanda Tana Kiwon Shanu

Kyakkyawar Santaleliyar Budurwa Ta Ba da Mamaki, an Ganta Rike da Sanda Tana Kiwon Shanu

  • Wata kyakkyawa kuma tsaleliyar budurwa ta bayyana a gidan gona, inda ta tsaya tare da wasu manyan shanu masu kaho
  • A bidiyon da ta yada a TikTok, Estella Kazi ta ce ya wuni a wani gidan gona mai suna Mburara, inda aka ajiye wasu bula-bulan shanu
  • Ya zuwa ranar 6 ga watan Janairu, an yi wa bidiyon dangwalen nuna sha’awa sama da 26k, kuma mutane da yawa sun yada da jarumtarta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

‘Yan TikTok sun shiga mamaki da yabon wata kyakkyawar budurwar da ta kai ziyara wani gidan gona, inda aka ganta tare da wasu shanu.

Budurwar mai suna Estella Kazi ta yada bidiyo a ranar 6 ga watan Janairu a TikTok, inda tace ta wuni a gidan gonan Mburara.

Shanun da aka gani a gidan gonan na Mburara a cike da koshe suke, kuma gasu da manyan kaho.

Kara karanta wannan

“Ta Yi Kama Da Shi”: Tsohuwa Da Ta Yi Kama Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ta Yadu a TikTok

Kyakkyawar budurwa a gidan gona ta ba da mamaki
Kyakkyawar Santaleliyar Budurwa Ta Ba da Mamaki, an Ganta Rike da Sanda Tana Kiwon Shanu | Hoto: TikTok/@estellakazi.
Asali: UGC

Bidiyon doguwa kyakkyawar budurwa tare da kafta-kaftan shanu

Kahon shanun da abin tsoro ne, inda mutane da yawa a kafar sada zumunta suka ce sun yi mamakin yadda take tafiya a tsakanin shanun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Estella ta nuna cewa, ba ta tsoron shanun, kuma an ga tana taba jikinsu lokacin da suke cin ciyawa suna tika.

Da gani dai shanun ba sa fada, domin kuwa sun dukufa suna tika, Estella na taba jikinsu.

Wani abin da ya ja hankalin jama’a a TikTok shine tsawon Estella, domin kuwa doguwa ce ainun.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’ar TikTok

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa game da ita:

@abbakarmuhammad480:

"Ina matukar farin ciki."

@mashudulukhwareni:

"Doguwa kuma kyakkyawa."

@k2jfannix:

"Allah ya taimake ki."

@mustaphalatifi010:

"Nima makiyayi ne."

@bhekistrongteaspeedygama:

"Ina son mata masu jajircewa kamar ki"

@umargashash:

"Ina kaunarki ‘yar uwa.”

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Aikatu A Gidansu Saurayinta Don Neman Gindin Zama, Bidiyon Ya Yadu

@dkim81777:

"Wannan na daya daga cikin mafarkaina. Ina kaunar kiwo sosai"

@patykhatala:

"Wadannnan kyawawan dabbobi ne.”

@famousmo5:

"Ina son tsawonki.”

Aure Shine Babbar Nasarata, Na Ga Tsiya Lokacin da Nake Layi, Inji Wata Mata

A wani labarin kuma, wata mata ta ce ta sha fama a lokacin da take layi; kafin ta yi aure ta shuga daga ciki.

A cewarta, mutane sun sha yi mata maganganun da basau da dadi kawai don bata da aure, amma yanzu ya wuce.

Ta shaida cewa, babban nasarar da ta samu a rayuwarta itace yin aure, don haka tana mutunta lamarin da ya shafi aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel