Mahaifi Ya Sadaukar Da Rayuwarsa Don Ceto Ran Dansa Yayin Da Gini Ya Rufta Musu

Mahaifi Ya Sadaukar Da Rayuwarsa Don Ceto Ran Dansa Yayin Da Gini Ya Rufta Musu

  • Wani mahaifi ya rasa ransa wurin kare dansa lokacin da gini ya fado a kansu yayin da ake tafka ruwan sama a jihar Ondo
  • An samu gawar marigayin mai suna Titus Adega a kife a kan dan nasa bayan rugujewar gini a kansu
  • Matar marigayin mai suna Margaret Adega ta ce ta fito yayin da ake tafka ruwan ta samu gawar mijinta a kan dan nasu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Wani mutumi mai suna Titus Adega ya rasa ransa yayin kare dansa lokacin da ake tafka ruwa kamar da bakin kwarya a jihar Ondo.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata 1 ga watan Agusta da misalin karfe 3:00 na yamma a Obale da ke karamar hukumar Akure ta Arewa.

Mahaifi ya rasa ransa yayin ceto dansa daga rugujewar gini a jihar Ondo
Wani Mahaifi Ya Rasa Ransa A Kokarin Ceto Dansa Daga Ruftawar Gini. Hoto: Punch.
Asali: UGC

Wata 'yar haya a gidan, Elizabeth Columbus ta ce wani bangare na ginin ya fado a kan Titus da dansa mai shekaru 5 mai suna Kizito Adega, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Tsere A Gidan Kaso Watanni 4 Kafin Wa'adinsa, Ya Shiga Tasku Bayan Kama Shi Da Kara Masa Shekaru 40

Yadda mahaifin yaron ya rasa ransa a kokarin ceto shi

Matar marigayin, Margaret Adega ta ce ginin ya fado a kan mijinta da dan nasu yayin da suke waje a lokacin da ake tafka ruwan saman, cewar Vanguard.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta:

"Na jiyo ihun yaron ina cikin bacci, na fito da gudu na same su a cikin tarkacen ginin.
"Na yi kokarin tono shi kawai sai na ga miji na a kansa, na tabbatar ya yi haka ne don kare shi lokacin da ginin ya rufta."

Matar ta bayyana yadda ta nemi taimakon makwabta don zakulo shi

Ta kara da cewa:

"Na nemi taimakon makwabta inda suka taya ni tsamo su daga cikin ginin tare da kai su asibiti.
"A asibitin a ka ce mana mu dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa inda a can aka tabbatar ya rasu."

Kara karanta wannan

Rikici Yayin Da Wata Mai Koyon Sana’a Ta Tsere Da Jinjirin Uwar Dakinta Dan Kimanin Watanni 2 A Wurin Biki, An Bazama Nemanta

Matar ta ce da zarar an sallami dan nata daga asibiti za a dauki gawar Adega zuwa jihar Benue don binne shi, cewar Tori News.

Tankar Mai Ta Fashe A Jihar Ondo, Ta Halaka Mai Juna Biyu Da Wasu 157

A wani labarin, fashewar tankar dakon mai a jihar Ondo ta yi ajalin mutane fiye da 15.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Odigbe da ke jihar inda wata mata mai juna biyu abin ya rufta da ita.

Rahotanni sun tabbatar cewa hakan ya faru ne yayin da mutane su ka je dibar ganimar man fetur daga tankar mai din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.