Tankar Dakon Mai Ta Fashe a Jihar Ondo, Ta Halaka Mai Juna Biyu da Wasu Sama da 157

Tankar Dakon Mai Ta Fashe a Jihar Ondo, Ta Halaka Mai Juna Biyu da Wasu Sama da 157

  • Wata Tankar dakon man fetur da ta yi hatsari a jihar Ondo, ta fashe kuma ta kama da wuta yayin da mutane ke ɗibar ganima
  • Rahoto ya nuna cewa wata mata mai juna biyu, kananan yara uku da wasu sama da mutum 15 ne suka rasa rayukansu a wurin
  • Mahukunta sun ɗauki dukkan waɗanda lamarin ya shafa zuwa Asibiti, an kwantar da waɗanda suka ji raunuka

Ondo state - Wata mata mai juna biyu da yara uku na daga cikin wadanda suka kone kurmus a ranar Lahadi bayan da wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a garin Ore da ke karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.

An ce fashewar ta afku ne a lokacin da wadanda abin ya shafa suka garzaya domin dibar ganimar man fetur daga Tankar, wacce ta sauka daga titi kuma ta yi hatsari.

Kara karanta wannan

"Abin Ya Fara Isa Ga Kowa Yanzu": Bidiyo Ya Nuna Ayarin Motoccin Gwamnan Najeriya Ta Makale Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ya Mamaye Titi

Taswirar jihar Ondo.
Tankar Dakon Mai Ta Fashe a Jihar Ondo, Ta Halaka Mai Juna Biyu da Wasu Sama da 157 Hoto: Punchng
Asali: UGC

Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilin jaridar Daily Trust cewa gobarar ta tashi ne biyo bayan tartsatsin wayar salula ta daya daga cikin wadanda ke diban mai a wajen.

Yadda lamarin ya yi ajalin rayuwa sama da 15

Wani ganau mai kasuwanci a yankin, Mista Bamidele, ya ce tun da farko masu ababen hawa da ke wuce wa sun gargadi wadanda abin ya shafa da kada su kuskura su matsa kusa da tankar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoton Punch, ya ce:

"Ina kokarin sallamar wani kwastoma na sai naga direban na kokarin sarrafa tankar dakon man, daga ƙarshe abin ya fi karfinsa ya sauka daga kan titi, motar ta yi haɗari. Ganin haka mutane suka cika wurin ɗauke da jarkoki."
"Wasu direbobi da fasinjoji da suka ga abinda ya faru sun gargaɗi mutane kar su je kusa da tankar amma suka ƙi ji. Ba zato muka ji ta fashe, daga baya muka samu labari wayar salula ce ta haddasa fashewar."

Kara karanta wannan

Jihar Kano Na Kan Gaba a Yawan Wadanda Suka Kamu Da Cutar Mashako a Najeriya

"Mace mai juna biyu, kananan yara uku da wasu mutane sama da 15 ne suka rasa rayukansu sanadin fashewar tankar dakon man Fetur ɗin."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Bamidele ya ƙara da cewa hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta ɗauke gawar waɗanda suka mutu da sauran waɗanda suka tsira zuwa Asibitin gwamnati.

Kwamandan FRSC reshen jihar Ondo, Mr Ezekiel SonAllah, ya tabbatar da lamarin inda ya ce waɗanda suka tsira na kwance ana masu magani a Asibiti.

Haka zalika, kakakin yan sandan Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun ƙone ƙurmus, an kai su ɗakin aje gawa.

Shugaba Tinubu Ya Sake Magana Mai Jan Hankali Kan Matsalar Tsaron Najeriya

A wani labarin na daban kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙara jaddada kudirinsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

A wurin bikin yaye sojoji a Jaji, jihar Ƙaduna, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa zata ba da fifiko a ɓangaren yaƙi da masu ta da ƙayar baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel