Hukumar NEMA Ta Kara Tsaurara Tsaro a Rumbun Abincinta Na Kaduna Bayan Wawason Da Aka Yi a Adamawa

Hukumar NEMA Ta Kara Tsaurara Tsaro a Rumbun Abincinta Na Kaduna Bayan Wawason Da Aka Yi a Adamawa

  • Hukumar NEMA ta bayyana bukatar jami’an tsaro da su taya su gadin dakin ajiyar kayan abinci da suke dashi a jihar Kaduna
  • Wannan ya biyo bayan fasa dakin ajiyar abinci na NEMA da wasu jama’a suka yi a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da dandana wahala da zafin cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi kwanan nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta yi kira ga jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da ‘yan sanda da kuma rundunar sojojin Najeriya da su tsare ma’ajiyarta a jihar Kaduna.

Kodinetan ofishin NEMA na shiyyar Kaduna, Abbani Imam, wanda ya bayyana hakan, ya danganta lamarin da abin da ya faru a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Innalillah: 'Yan bindiga sun kashe babban malamin Izala da wasu 5 a jihar Kaduna

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu jama’a suka kutsa cikin dakin ajiyar NEMA da ke Adamawa tare da wawashe kayan abinci da nufin rage wa kansu radadin cire tallafin man fetur.

NEMA na neman tallafin sojoji wjajen kare rumbunta
NEMA ta nemi taimakon sojoji a Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Muna neman agajin sojoji da DSS, inji NEMA

Imam ya bayyana cewa sun samu umarnin su tuntubi jami’an tsaro, musamman ma jami’an da ke rage radadin iftila’i (DRUs), wanda ya shafi dukkanin hukumomin tsaro don hada kai da NEMA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Mun tuntubi jami’an ‘yan sanda na yanki (DPOs) a inda ma’ajiyarmu suke domin mu kasance a ankare. Mun kuma sanar da dukkan jami’an SSS kuma muna sa ido sosai kan lamarin.”

Imam ya jaddada cewa suna sa ido kan lamarin a cikin gida kuma za su sanar da masu ruwa da tsaki duk wani hali da mafita da aka samu, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilan da Suka Jawo Babu Minista ko 1 Daga Kano, Filato da Legas a Sahun Farko

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 domin duba lamarin da ya faru na fasa dakin ajiyar na NEMA.

Yadda matasa suka fasa rumbun abinci na dan majalisa

A wani labarin kuma, buhunan masara da shinkafa na daga cikin kayayyakin da aka sace a wani dakin ajiyar kaya da ke Jalingo babban birnin jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ce wasu gungun jama'a ne suka kutsa kai tare da aikata wannan barna a cikin makon da ya gabata.

Tun bayan cire tallafin man fetur mutane da yawa a Najeriya suka shiga dimuwa tare da fara neman hanyar da za su rage radadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel