Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari dakin ajiyan hukumar kwastam, sun kwashe buhuhunan shinkafa

Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari dakin ajiyan hukumar kwastam, sun kwashe buhuhunan shinkafa

- Daga zanga-zanga, wasu matasa sun fasa fashin kayan abinci a rumbun gwamnati

- Matasa a jihar Edo sun saba dokar ta bacin da gwamnatin jihar ta sa

- Jiya bata gari a jihar suka fasa gidajen yari biyu kuma suka kari fursunoni kimanin 2000

Wasu bata gari a ranar Talata sun fasa dakin ajiyar hukumar hana fasa fasa kwabri watau Kwastam dake garin Benin City da sunan zanga-zangan #EndSARS.

An tattaro cewa bata garin sun fasa dakin ajiyan dake Ikpoba da yammacin Talata kuma sukayi awon gaba da kayayyakin abinci da wasu kayayyaki, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika an tattaro cewa mutan unguwa suka samu labarin abinda ke faruwa, sun garzaya wajen domin samun nasu rabon na kayan masarufin.

An ga bata garin da mazaunan suna awon gaba da buhuhunan shinkafa da was kayayyaki.

Yumkurin tuntubar kakakin hukumar yan sandan jihar, Chidi Nwanbuzor, ya ci tura.

KU KARANTA: EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari dkin ajiyan hukumar kwastam, sun kwashe buhuhunan shinkafa
Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari dkin ajiyan hukumar kwastam, sun kwashe buhuhunan shinkafa Hoto: Makarantar kwastam
Asali: Twitter

DUBA NAN: EndSARS: Buhari ya gana da ministan tsaro tare da shugaban tsaro

Matasan sun kai wannan hari ne duk da cewa gwamnatin jihar ta sanya dokar ta baci a jihar.

Mun kawo muku cewa gwamnatin jihar Edo ta sanar da sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a fadin jihar. Dokar za ta fara aiki daga karfe 4:00pm na ranar 19 ga watan Oktoba, har sai baba-ta-gani.

Babban sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie ne ya fitar da sanarwar, Channels TV ta ruwaito.

Ogie ya bayyana cewa an sanya takunkumin ne sakamakon hare-haren da wasu yan iska da suka mamaye zanga-zangar #ENDSARS suka aiwatar.

Hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya (NCS) ta tabbatar da cewa fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin da ma su zanga-zanga su ka balle ranar Litinin a Benin, jihar Edo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel