Mutanen El-Rufai Sun Dawo Cikin Sababbin Kwamishonin Gwamna Uba Sani a Kaduna

Mutanen El-Rufai Sun Dawo Cikin Sababbin Kwamishonin Gwamna Uba Sani a Kaduna

 • Gwamna Uba Sani zai kafa majalisar FEC, ya aikawa ‘yan majalisar dokoki jerin Kwamishinoni
 • Duka-duka akwai sunayen mata hudu da kuma maza tara da ake sa ran za su samu mukami a SEC
 • Za a ba Farfesa Muhammad Sani Bello da Rt. Hon. Abdullahi Aminu Shagali PhD kujera a Kaduna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya aikawa majalisar dokoki sunayen wadanda yake so a nada a matsayin sababbin Kwamishononi.

Legit.ng Hausa ta fahimci takardar Mai girma Gwamnan ta shiga hannun ‘yan majalisar ne a safiyar yau da aka dawo aiki a majalisar Kaduna.

Sunayen wadanda aka za a nada sun hada da Farfesa Muhammad Sani Bello wanda shi ne shugaban kwamitin yakin neman takarar Uba Sani a APC.

El-Rufai
Sunayen Kwamishinonin Kaduna Hoto: Legit.ng Hausa
Asali: Original

An dauko Shagali da Mamman Lagos

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Kwamishinoni 24 Da Gwamnan Bauchi Ya Aikawa Majalisar Dokokin Jihar

Wani wanda ya yi wa Gwamna Sani kamfe da ya samu shiga shi ne Sadiq Mamman Lagos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jerin akwai Rt. Hon. Abdullahi Aminu Shagali wanda ya taba rike shugabancin majalisa dokoki da kuma mai ba Gwamnatin El-Rufai shawara.

Akwai Umma Kaltume Ahmed wanda tayi aiki a matsayin Kwamishina, magajiyar gari da kuma Darekta Janar a lokacin Malam Nasir El-Rufai.

Wani tsohon Kwamishina da ya dawo shi ne Arch (Dr.) Ibrahim Hamza, wanda ya shugabanci ma’aikatar ruwa da hukumar KADFAMA a baya.

Ragowar sun hada da Salisu Rabi Hajia, Patience Fakal da Abubakar Buba da malamin jami’a kuma ‘dan APC, Farfesa Benjamin Kumal Gugong.

Murtala Mohammad Dabo wanda yana cikin masu ba El-Rufai shawara kan harkar tattalin arziki zai samu shiga cikin gwamnatin Sanata Uba Sani.

 1. Umma Khultume Ahmed
 2. Mukhtar Ahmed
 3. Arch. Dr. Ibrahim Hamza
 4. Sule Shu’aibu
 5. Auwal Musa Shugaba
 6. Shizzer Nasara Joy Bada
 7. Farfesa Muhammad Sani Bello
 8. Farfesa Benjamin Kumal Gugong
 9. Salisu Rabi Hajia
 10. Patience Fakal
 11. Abubakar Buba
 12. Saddiq Mamman Lagos
 13. Murtala Mohammad Dabo
 14. Abdullahi Aminu Shagali.

Kara karanta wannan

Lambar Ministan Buhari Ta Fito, Gwamnatin Tinubu Za Ta Bincike Shi Kan Abubuwa 5

"A shirya ganin sauyi a ma'aikata"

Aminu Baba Doko yana cikin 'ya 'yan APC kuma mabiyan Aminu Shagali a Zariya, ya fada mana cewa idan mai gidansu ya shiga ofis, za a ga canji.

"Na san Hon. Aminu Shagali zai kawo gyara sosai saboda gogewarsa a matsayin tsohon shugaban majalisa da mai bada shawara a harkar siyasa.
Zai kawo sauyi a duk ma'aikatar da za a tura shi a matsayin Kwamishina a Kaduna."

- Aminu Baba Doko

Siyasar Majalisar Tarayya

Rahoto ya zo cewa Rt. Hon. Tajudeen Abbas zai yi fama da ‘Yan majalisa wajen kason kwamitocin majalisar tarayya, akwai yiwuwar akwai kura kan teburinsa.

Kusoshin a majalisa sun fusata, su na zargin an saba alkawarin da aka yi kafin su janye takara domin ana zargin ‘yan majalisar Legas sun kwashe mukami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel