Yamutsi a Majalisa, Yarbawa Sun Tashi da Manya-manyan Kwamitoci da Ake ji da Su

Yamutsi a Majalisa, Yarbawa Sun Tashi da Manya-manyan Kwamitoci da Ake ji da Su

  • Bisa dukkan alamu za ayi gumurzu a wajen rabon kwamitocin majalisar tarayya a cikin makon nan
  • Shugaban majalisar wakilai ba ya Najeriya a halin yanzu, amma nan da Alhamis za a raba kwamitoci
  • Legas ta samu mafi yawan kwamitocin da ake ganin su na da tsoka, sauran ‘yan majalisa na korafi

Abuja - Yayin da ake shirin rantsar da kwamitocin majalisar tarayya, an samu rashin jituwa saboda yadda aka yi rabon mukaman da ake rububi.

Leadership ta kawo rahoto cewa an samu sabani a majalisar wakilai da majalisar dattawa a karshen makon jiya, wasu su na kukan rashin adalci.

Zargin da ake yi shi ne masu rike da madafan iko a fadar shugaban kasa su na da hannu wajen yadda aka yi rabon kwamitocin majalisar kasar.

Rikici a Majalisa
Shugabannin Majalisar Tarayya Hoto: @ngrspeakerabbas
Asali: Twitter

Za a sanar da shugabannin kwamitoci

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kakakin Majalisar Wakilai Zai Gana Da Tinubu, Cikakken Bayani Ya Bayyana

Zuwa ranar Alhamis za a sanar da yadda aka yi rabon kwamitoci a majalisun wakilai da dattawa, daga nan ne za a tafi hutun makonni shaida.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sabanin ya fi yawa a majalisar wakilan tarayya inda ake da ‘yan siyasa kusan 360 da jiga-jigan ‘yan majalisa su ka ji labarin abin da ke faruwa.

Rahoton ya ce wani daga cikin ‘yan majalisar ya ce an fifita ‘yan siyasan Legas da yaransu wajen raba mukaman, an ba su manyan kwamitoci.

Kudu maso yamma

Majiyar ta ce ‘yan majalisar Legas za su rike shugabancin kwamitocin tattalin arziki, tsaro, masana’antu da kwamitin ayyukan ‘yan majalisa.

Babajimi Benson mai wakiltar Ikorodu zai rike kwamitin tsaro, Tasir Wale Raji mai wakiltar Epe zai shugabanci kwamitin ayyukan majalisar kasar.

Muktar Betara bai ji dadi ba

Kara karanta wannan

A Kurarren Lokaci, Tinubu Ya Cire Mutum 4 a Jerin Wadanda Za A Ba Kujerar Minista

‘Dan majalisar Ondo, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ake so ya jagoranci kwamitin ayyuka wanda aka yi wa Hon. Muktar Betara tayi, amma sai ya ki karba.

Jaridar ta ce Muktar Betara yana a dawo masa da kujerar shugaban kwamitin kasafin kudi, amma ana maganar Abubakar Kabir Bichi ake hari.

Sannan an warewa ‘dan majalisar Oyo, Akeem Adeyemi shugabancin kwamitin noma, wannan ya fusata ‘yan majalisar da suka fito daga Arewa.

Kanwar Mujaheed Asari-Dokubo, Hon. Boma Goodhead za ta rike kwamitin harkokin Neja Delta.

Aikawa Majalisa sunayen Ministoci

Kun samu labari cewa watakila yau ko gobe a karanto takardar shugaban kasa a Majalisa, a ji wadanda ake so a ba Minista a gwamnatin tarayya.

Tsofaffin Gwamnonin da su ka taka rawar gani a zaben 2023 sun kasa sun-tsare a fadar Aso Rock. Hankali ya karkata zuwa Jihohin Ribas da Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel