An Shiga Tashin Hankali Da Jimami Kan Bullar Wata Bakuwar Cuta a Jihar Kaduna

An Shiga Tashin Hankali Da Jimami Kan Bullar Wata Bakuwar Cuta a Jihar Kaduna

  • An samu ɓullar wata baƙuwar cuta a garin Kafanchan na jihar Kaduna wacce ta salwantar da rayukan mutum huɗu
  • Cutar wacce ba a san kowace iri ba ce dai ta janyo an kulle dukkanin makarantun dake a garin na ganin Kafanchan
  • An yi bayanin alamomin cutar tare da kira ga iyaye da sun lura da alamomin a jikin yaransu da su gaggauta zuwa asibiti

Kafanchan, Jihar Kaduna - Wata baƙuwar cuta da ta ɓulla a garin Kafanchan, hedkwatar ƙaramar hukumar Jama'a a jihar Kaduna, ta yi sanadiyyar salwanyar rayukan mutum.

Jaridar Aminiya ta kuma bayyana cewa ɓullar cutar ta sanya an killace wasu mutum 10 a babban asibitin tunawa da Patrick Yakowa da ke a garin na Kafanchan.

Bakuwar cuta ta bulla a jihar Kaduna
Marasa lafiya a asibitin Kafanchan Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

Ɓullar cutar ta sanya an kulle makarantu a garin na Kafanchan bayan hukumomi sun sallami ɗalibai ranar Alhamis da safe.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Babban sakataren asibitin, Ezra Joshua, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce tuni har an ɗauki samfurin cutar domin zuwa yin gwaji domin gano irin cutar a Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa sun killace mutum 10 waɗanda aka kawo musu a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis.

Joshua ya yi bayanin cewa cutar tana kama yara ne ƙanana masu shekara ɗaya zuwa 13 inda ta ke yi musu illa ba tare da ɓata lokaci ba tana kama su.

Yadda alamomin cutar su ke

Joshua ya bayyana cewa baƙuwar cutar tana da alamomin dake farawa da zazzaɓi, ciwon maƙogwaro, mutuwar jiki da kasala.

Babban sakataren asibitin ya kuma gargaɗi iyaye da su daina alaƙanta cutar da ciwon daji ko zuwa wajen masu maganin gargajiya, inda ya shawarce su da gaggauta kawo duk yaron da suka lura da alamomin cutar a tattare da shi.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Batun Ciyo Bashin Biliyan 10 Don CCTV, Ya Fayyace Gaskiyar Al'amari

Shugaban ƙaramar hukumar Jama'a, Mr. Yunana Barde ya yi kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Cutar Anthrax Ta Bulla a Neja

A wani labarin na daban kuma, gwamnatin tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar 'Anthrax' mai yin kisa a jihar Neja.

Hukumomi sun tabbatar da cewa cutar ta ɓulla ne a wani gidan gona dake a garin Suleja na jihar Neja. Ma'aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta yi bayanin cewa an samu wasu shanu ne a gidan gonan da suka nuna alamun cutar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel