Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar 'Anthrax' Ta Farko a Neja

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar 'Anthrax' Ta Farko a Neja

  • Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bullar cutar 'Anthrax a wani gidan gona da ke jihar Neja
  • Hadin gwiwar jami'an lafiya na Gwamnatin Tarayya da na jihar Neja ne suka tabbatar da hakan bayan gudanar da bincike
  • Gwamnatin Najeriya ta shawarci 'yan kasar da su yi gaggawar kai rahoto a duk lokacin da suka ga wani dauke da alamomin cutar

Niger - Gwamnatin Tarayyar ta tabbatar da ɓullar cutar nan mai kisa wato 'Anthrax' a ƙasar.

Wata sanarwa da ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Dr. Columba T. Vakuru, babban jami’in kula da lafiyar dabbobi na Najeriya, ce ta bayyana hakan.

Sanarwar ta ce an samu dabbobin da ke nuna alamun yiwuwar kamuwa da cutar ta 'Anthrax' a wani gidan gona da ke Suleja, jihar Neja kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jam'iyyar APC Ya Ɗau Zafi, Ta Ɗage Muhimman Taruka 2 Bayan Murabus Ɗin Adamu

Gwamnatin Tarayya ta sanar da bullar cutar Anthrax ta farko
Gwamnatin Tarayyar ta ce an samu bullar 'Anthrax' a Neja. Hoto: News Medical
Asali: UGC

Sanarwar ta ƙara da cewa a gidan gonar akwai dabbobi daban-daban da suka haɗa da shanu, tumaki da awaki, wacce take a Gajiri da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Columba ya ce jami'an lafiya na tarayya da na jiha sun je gidan gonar inda suka ɗauki samfurin gwaji daga jikin dabbobin.

Ya ƙara da cewa an gudanar da gwaje-gwaje kan samfuran inda daga nan ne aka tabbatar da cewa dabbobin suna ɗauke da ƙwayoyin cutar ta 'Anthrax'.

Gwamnati ta gargaɗi 'yan Najeriya game da cutar ta 'Anthrax'

Dama Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ‘yan Najeriya makonnin da suka gabata bayan samun labarin ɓarkewar cutar ta Anthrax a Arewacin Ghana, inda duka dabbobin da suka kamu da cutar suka mutu.

An bayyana cewa wata ƙwayar halitta ta bakteriya mai suna 'Bacillus', wacce ke ke kama dabbobi irinsu shanu, tumaki da kuma awaki.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Cafke ‘Yan Bindiga Daga Dawowa Daga Hajji a S/Arabiya

Sai dai cutar za ta iya yaɗuwa zuwa mutane a yayin da suka cuɗanyu da mutane masu cutar ko kuma idan sun yi mu'amala da dabbobin da ke ɗauke da cutar.

Gwamnatin Tarayya ta bukaci 'yan Najeriya su kai rahoton ɓullar cutar ta 'Anthrax'

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga 'yan Najeriya da su yi gaggawar kai rahoto a duk lokacin da suka ga wata dabba da ta nuna alamomin cutar.

Daga cikin manyan alamomin cutar akwai fitar jini daga ƙofofin jikin dabba ko mutane. Haka nan kuma cutar na shafar numfashi a jikin mutane.

Sannan an buƙaci 'yan Najeriya da su riƙa daukar matakan killace dabbobin da suka nuna alamar kamuwa gabanin kai rahoto zuwa cibiyoyin kula da dabbobi mafi kusa kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Likitoci sun ceto rayuwar wani yaro da kansa ya kusa rabewa biyu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan wani yaro ɗan ƙasar Falasɗin da likitocin Isra'ila suka ceto a lokacin da kansa ya kusa rabewa biyu.

Kara karanta wannan

Za a rina: Fitacciyar jami'a ta zama ta 2 mafi nagarta a Najeriya, shugabanta ya magantu

Lamarin ya faru ne a lokacin da mota ta ture yaron a yayin da yake tafiya a kan keke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel