Ganduje Ya Yi Magana Kan Bashin Biliyan 10 Na Aikin Kyamarar Tsaro Ta CCTV a Kano

Ganduje Ya Yi Magana Kan Bashin Biliyan 10 Na Aikin Kyamarar Tsaro Ta CCTV a Kano

  • Gwamnatin Kano da ta shuɗe, ta yi martani kan zargin da ake mata na cewa ta ciyo bashin naira biliyan 10 domin sanya CCTV a cikin babban birnin jihar
  • A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 18 ga watan Yuli, tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zargin ba gaskiya ba ne
  • Sai dai ya bayyana cewa, Majalisar Dokokin jihar Kano a lokacin ta amince da a ciyo bashin, amma wata babbar kotun tarayya da ke jihar ta dakatar da batun

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta samu rancen naira biliyan 10 domin sanya kyamarorin tsaro na CCTV a cikin birnin.

A wata sanarwar da ya fitar ranar Talata, ta hannun Malam Muhammad Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na lokacinsa, Ganduje ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Masoyin Tinubu Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, Ya Yi Iƙirarin Daukar Mummunan Mataki

Ganduje ya musanta batun ciyo bashin naira biliyan 10
Ganduje ya karyata batun ciyo bashin naira biliyan 10 don sanya kyamarorin CCTV. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Ya ce ana so a ɓata sunan Ganduje ne kawai

A cewar Malam Garba, wata kungiyar farar hula ce ta tado da batun domin kawai ta ɓatawa tsohon gwamnan suna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƙungiyar wacce ya ce ba ta a zahiri, an ɗauko hayarta ne kawai domin hakan, kuma suna yin duk waɗannan abubuwan ne don biyan buƙatun iyayen gidansu.

A dalilin hakan ne Malam Garba ya ce sun ƙalubalanci ƙungiyar da ta kawo musu hujjar cewa an ciyo kuɗaɗen da suke iƙirari a lokacin mulkin Ganduje kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kotu ce ta hana Ganduje karɓo bashin na naira biliyan 10

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Majalisar Dokokin jihar Kano ta wancan lokacin, ta bai wa gwamnatin Ganduje izinin ciwo bashin domin aiwatar da aikin sanya kyamarorin tsaron da su.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Sai dai wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a cikin birnin Kano, ta yanke wani hukunci da ya hana gwamnatin ta Ganduje karɓo rancen waɗannan kuɗaɗe kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Malam Garba ya ƙara da cewa gwamnatin ta Ganduje ta so aiwatar da wannan gagarumin aiki, musamman ma domin samar da tsaro a birnin na Kano, sai dai har wa'adinta ya ƙari ba ta samu ikon yin hakan ba.

Abba Gida Gida ya naɗa masu bashi shawara kusan mutane 50

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa, gwamnan jihar Kano, Abba Gida Gida ya sanar da naɗin ƙarin masu ba shi shawara na musamman.

Hakan dai ya biyo bayan amincewa da Majalisar Dokokin jihar ta Kano ta yi kan buƙatar gwamnan na ƙara wasu hadiman su 25.

Asali: Legit.ng

Online view pixel