Mai Shari'a Ugo: Babban Alkali a Karar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkali a Karar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wani batu kan murabus ɗin mai shari'a Boloukuoromo, alƙali a kotun ɗaukaka ƙara na ci gaba da yaɗuwa a soshiyal midiyal
  • Lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an fitar da wata jita-jita akan alƙalin alƙalai na ƙasa, Olukayode Ariwoola
  • Batun cewa mai shari'a Ugo ya fitar da sanarwa kan goyon bayan Tinubu da yin murabus, ƙirƙirarsa kawai aka yi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara a ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, ta musanta rahoton cewa ɗaya daga cikin alƙalai biyar, mai shari'a Boloukuorom Ugo, da ke jagorantar ƙarar neman a soke nasarar Tinubu, ya yi murabus.

Wani babban jami'i a kotun wanda ya yi magana da jaridar Vanguard, ya bayyana rahoton a matsayin labarin ƙarya, inda ya yi nuni da cewa aikin masu yaɗa jita-jita ne kawai.

Kara karanta wannan

Shaidan PDP Ya Dabarbarce a Gaban Kotu, Ya Yi Magana Daga Baya Ya Warwareta

Ba gaskiya ba ne batun murabus din mai shari'a Ugo
Batun cewa mai shari'a Ugo ya yi murabus karya ne Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Shin mai shari'a Ugo ya fitar da sanarwa kan zargin ana ƙoƙarin yi wa shari'ar karan tsaye? Gaskiya ta bayyana

Majiyar wanda ya nemi da a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana da ƴan jarida ba, ya ce babu makamancin hakan da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ina tabbatar maka da cewa babu wani abu makamancin hakan. Maganar gaskiya ita ce mun kaɗu lokacin da mu ka ji wannan labarin ƙaryan."
"Na yi amanna cewa idan har ba wani aka hukunta ba, wannan yawaitar yaɗuwar labaran ƙaryar zai ci gaba ne."

Haka kuma, a wani rahoton da cibiyar FIJ ta fitar, ya ƙaryata batun cewa mai shari'a Ugo ya fitar da sanarwa yana zargin yunƙurin yi wa doka karan tsaye a shari'ar zaɓen shugaban ƙasan da ake yi.

FIJ ta bayyana cewa batun ya samu asali ne daga The Igbo Times Magazine, wata jaridar yanar gizo wacce ta yi fice a wajen wallafa labarai kan al'adar ƙabilar Inyamurai da yin batutuwa waɗanda ba ƙamshin gaskiya a cikinsu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Kira Alkalin Alkalai Na Kasa Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasa? Gaskiyar Zance Ya Bayyana

A cewar The Igbo Times Magazine, Ugo ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa an bukace shi da ya taka doka ta hanyar yin hukunci wanda zai taimaki wani ɗan takara, wanda bai bayyana sunansa ba, amma ake ganin cewa Bola Tinubu ne.

Sai dai binciken da Vanguard da FIJ suka yi, ya nuna cewa babu wasu bayanai a hukumance da ke tabbatar da cewa mai shari'a Ugo ya yi murabus.

Saboda haka, batun cewa Ugo ya fitar da sanarwa yana zargin cewa an yi masa daɗin baki ya taka doka a shari'ar ƙarya ne.

Gaskiyar Zance Kan Nada Al-Mustapha Shugaban Hukumar DSS

A wani labarin kuma, an bayyana gaskiyar zance kan labaran da ke yawo cewa Shugaba Tinubu, ya naɗa tsohon babban dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, shugaban hukumar DSS.

Binciken da aka gudanar ya bayyana cewa ƙarya ce kawai tsagwaronta masu yaɗa labaran suka zauna suka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel