Yan Bindiga Sun Tare Amarya Da Kawayenta Ranar Daurin Aure a Jihar Neja

Yan Bindiga Sun Tare Amarya Da Kawayenta Ranar Daurin Aure a Jihar Neja

  • Ƴan bindiga sun yi ƙokarin sace wata amarya tare da ƙawayenta suna kan hanyarsu ta sada ta da gidan miji
  • Amaryar dai ta yi ta maza ta tube rigar amarci inda ta ranta ana kare cikin daji domin tsira daga faɗa wa hannun ƴan bindigan
  • Ƴan bindigan sun sace biyu daga cikin ƙawayen amaryar amma sun samu sun kuɓuta daga hannun miyagun daga baya

Jihar Neja - Wata amarya a jihar Neja ta sha da ƙyar lokacin da ƴan bindiga suka kai musu farmaki ita da ƙawayenta ana kan hanyar kai ta gidan miji.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa amaryar ta tuɓe rigar amarcinta inda ta ranta ana kare ta yi tafiya mai nisa a cikin daji domin tserewa daga shiga hannun ƴan bindigan.

Yan bindiga sun tare amarya a jihar Neja
Amaryar ta sha da kyar a hannun 'yan bindiga Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Amaryar dai an ɗauko ta ne daga wani ƙauye cikin ƙaramar hukumar Paikoro zuwa Kuta, hedikwatar ƙaramar hukumar Shiroro, lokacin da ƴan bindigan suka kai musu farmaki a kusa da Kaffin-Koro cikin ƙaramar hukumar Paikoro.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Yadda ƴan bindigan suka so sace amaryar da ƙawayenta

Wata ƴar uwar amaryar wacce ta nemi da a sakaya sunanta, ta bayyana cewa suna cikin tsaka da tafiya ne kawai kafin su ankara sai ƴan bindigan suka kawo musu hari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamanta:

"Za mu kai amaryar Kuta ne daga ƙauyenmu. Lokacin da muka kusa zuwa Kaffin-Koro, sai ƴan bindiga suka kawo mana hari."
"Ƴar uwa ta tana sanye da rigar amare a ɗaya daga cikin motocin da ke a bayan mu. Nan da nan ta tuɓe ta. Ƴan bindigan sun bi mu da gudu cikin daji. An sace biyu daga cikin ƙawayen amaryar amma sun kuɓuta daga baya."
"Dole shagulgulan biki suka tsaya cak. An ɗage bikin sai wani lokacin."

Amaryar da angon dai sun ƙi su ce wani abu dangane da lamarin, amma wasu majiyoyi na kusa da su sun bayyana cewa sun shiga cikin tashin hankali.

Kara karanta wannan

Masha Allah: Dakarun Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace

'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Basarake

A wani labarin kuma wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a fadar basaraken Nguru a ƙaramar hukumar Aboh Mbaise da ke a jihar Imo.

Ƴan bindigan sun harbe basaraken mai martaba James Eze Nnamdi har lahira a harin da suka kai a fadarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel