Gwamnanmu Babu Lafiya, Yana Asibiti Bai Iya Komai Inji Shugaban APC, Adamu

Gwamnanmu Babu Lafiya, Yana Asibiti Bai Iya Komai Inji Shugaban APC, Adamu

  • Abdullahi Adamu ya tabo batun Rotimi Akeredolu wanda yake jinya a taron NWC da Shugabannin APC
  • Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya sanar da cewa rashin lafiyar Gwamnan ta yi kamari, ya yi masa addu’a
  • A wajen taron da aka yi a jiya, an yi maganar Shugaban APC da ‘yan bindiga su ka dauke a jihar Ekiti

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya yi magana a karon farko game da halin da Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu yake ciki.

This Day ta rahoto Sanata Abdullahi Adamu yana cewa Mai girma Rotimi Akeredolu yana kwance a asibiti, har ta kai ba zai iya tabuka komai a yanzu ba.

Shugaban APC mai-mulki na kasa ya yi wa wannan bayani ne a lokacin da shi da ‘yan majalisarsa ta NWC tayi zama da shugabannin jam’iyya na jihohi.

Kara karanta wannan

Kujerar Shugaban APC Na Tangal-Tangal Bayan Wata 15, Zai San Makomarsa a NEC

Jam'iyyar APC
Taron shugabannin jam'iyyar APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Kamar yadda aka sani, jam’iyyar APC ta tabbatar da halin rashin lafiyar da Gwamna Rotimi Akeredolu yake fama da ita, yana jinya a asibitin kasar waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai an hada da yin addu'o'i

Adamu ya yi addu’a ga Ubangiji ya ba Gwamnan na jihar Ondo lafiya domin ya dawo bakin aiki.

"A daidai wannan lokaci, mu na takaicin sanar da mummunan halin Gwamnan jihar Ondo na rashin iya tabuka komai kuma ya na jinya a kasar waje.
Mu na yi masa addu’a tare da yi masa fatan samun lafiya da gaggawa."

- Abdullahi Adamu

Kira ga shugabanni da Bola Tinubu

Rahoton ya ce shugaban na APC ya yi magana bukatar samun kyakkyawar alaka tsakanin Gwamnoni, shugabannin APC da majalisar NWC a kowace jiha.

A wajen taron Sanata Adamu ya yi kira ga Bola Tinubu da ya yi aiki da shugabannin jam’iyyarsu ta APC wajen zaben wadanda za su zama masa Ministocinsa.

Kara karanta wannan

Bayan Rigimar Majalisa, Rikicin Kuɗi Zai Kunno Kai Tsakanin Shugabannin APC

Rahoton Punch ya nuna a wajen wannan zama da aka yi a Abuja, an yi maganar shugaban APC na reshen jihar Ekiti wanda aka yi garkuwa da shi kwanaki.

Adamu yake cewa sai a jiya ya samu labarin Paul Omotosho ya na hannun ‘yan bindiga.

Gwamnan jihar Ondo ya nemi karin hutu

A farkon makon nan ne labari ya tabbatar da cewa har yanzu Gwamnan jihar Ondo bai gama samu sauki ba, ya bukaci majalisa ta kara masa hutun yin jinya.

Yayin da yake cigaba da murmurewa a kasar waje, Akeredolu ya bar mulki a hannun mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa yayin da al’umma ke yi masa addu’o’i.

Asali: Legit.ng

Online view pixel