Kujerar Shugaban APC Na Tangal-Tangal Bayan Wata 15, Zai San Makomarsa a NEC

Kujerar Shugaban APC Na Tangal-Tangal Bayan Wata 15, Zai San Makomarsa a NEC

  • Alamu na nuna babu tabbacin Abdullahi Adamu zai cigaba da zama shugaban jam’iyyar APC
  • Akwai zargin da ke wuyan Shugaban APC na kasa na yin facaka da kudin da jam’iyya ta tara
  • Wasu su na so Sanata Adamu ya yi murabus saboda shi Musulmi ne, sai Kirista ya jagoranci NWC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A yayin da ake shirin yin taron majalisar koli na jam’iyyar APC, babu wanda zai iya dukan kirji, ya yi hasashen makomar Abdullahi Adamu.

Rahotanni cikinsu akwai daga Daily Trust da ke nuna shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu bai da tabbacin zama a kujerarsa.

Adamu wanda ya zama shugaban APC a watan Maris na 2022 ya na fuskantar matsin lamba, ta kai wasu su na neman ya daina jagorantar NWC.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labour Ta Yi Azarɓaɓin Faɗin Abin Da Zai Faru a Ƙarshen Shari'ar Obi Da Tinubu

Kujerar Shugaban APC
Shugabannin APC a Aso Rock Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

An yi 'facaka' da kudi

Babban zargin da ke kan wuyan tsohon Gwamnan na Nasarawa shi ne facaka da dukiyar jam’iyya, don haka ake neman ya sauka daga matsayinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai wadanda ke ganin ya kamata Sanata Adamu ya sauka daga kujerarsa ne saboda addini.

Ganin shugaban kasa da mataimakin shugaban na Najeriya duka musulmai ne, wasu su na so ne jam’iyyar APC mai-mulki ta koma karkashin kirista.

Amma da wani daga cikin shugabannin jam’iyyar ya zanta da manema labarai a asirce, ya shaida cewa babu mai iya cewa ga abin da zai faru.

...Addini, Ahmad Lawan

Wani abin da ke neman kawowa Adamu matsala a NWC shi ne rashin goyon bayan Bola Tinubu a zaben tsaida gwani, ya fi karkata ga Ahmad Lawan.

"Akwai wadanda ba su kaunar salon shugabancin Adamu, kuma akwai wadanda su ke neman kawo rashin zaman lafiya da hargitsi.

Kara karanta wannan

Gwamnanmu Babu Lafiya, Yana Asibiti Bai Iya Komai, Shugaban APC, Adamu

A wancan lokaci Adamu bai goyi bayan Tinubu ba, amma mu yi watsi da wannan saboda mun ci zabe, lokacin hada-kai ne yanzu.

Majiyar ta ce tun farko da ana shirin tsige shugaban jam’iyyar, Bola Tinubu ba zai nada George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya ba.

Taron da aka yi a sakatariya

Rahoto ya zo cewa saboda gudun ayi masa bore, shugaban APC na kasa ya kira taro da daukacin shugabanni na reshen jihohi, su ka yi zama a Abuja.

A karshen taron da aka yi a sakatariyar jam’iyya da ke birnin tarayya, shugabannin jihohi sun nuna sun yi amanna da kamun ludayin shugaban na su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel