Yan Bindiga Sun Kashe Limamin Coci, Sun Yi Awon Gaba Da Mutum 7 Ana Tsaka Da Bauta

Yan Bindiga Sun Kashe Limamin Coci, Sun Yi Awon Gaba Da Mutum 7 Ana Tsaka Da Bauta

  • Yan bindiga sun kashe wani limamin cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) sannan sun yi garkuwa da yan cocin bakwai yayin da suke tsaka da bauta a jihar Ogun
  • Yan bindigar sun farmaki cocin RCCG da ke Abule-Ori tsakar dare yayin da ake gudanar da bauta
  • Sai dai kuma jami'an tsaro sun ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a cocin ba tare da rauni ba sannan sun kashe dan bindiga daya

Jihar Ogun - Yan bindiga sun farmaki cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) yayin da suke tsaka da bauta, sun kashe fasto tare da garkuwa a yan cocin bakwai a jihar Ogun.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli, a Abule-Ori, a yankin karamar hukumar Obafemi Owode.

Kara karanta wannan

Yadda Magidanci Ya Kange Matarsa Tare Da Hana Ta Abinci Na Tsawon Shekaru Biyu a Wata Jihar Arewa

Dakarun rundunar So-Safe CORPS
Yan Bindiga Sun Kashe Limamin Coci, Sun Yi Awon Gaba Da Mutum 7 Ana Tsaka Da Bauta Hoto: OGUN STATE So-Safe CORPS
Asali: Facebook

Ganzallo ya ce da samun labarin mai cike da damuwa kan lamarin, sai jami'an rundunar So-Safe suka shiga aiki. Sun ceto yan cocin da aka sace ba tare da rauni ba sannan suka kashe mutum daya yayin aikin.

Shugaban rundunar So-Safe ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tawagar rundunar ta musamman, reshen Owode-Egba, karkashin jagorancin ACC Jimoh Rasaki Omoniyi, sun samu kira mai cike da damuwa cewa anyi garkuwa da wasu mambobin cocin Redeemed Christian Church of God, karkashin yankin Ogun, Abule-Ori a karamar hukumar Obafemi Owode sannan an kashe faston."

Ganzallo ya kara da cewar:

"An ceto mutanen bakwai ba tare da rauni ba yayin da aka kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen kuma mutane da dama sun jikkata a yayin musayar wuta."

Ya ci gaba da bayyana cewa jami'an yan sandan da na So-Safe suna bibiyar masu garkuwa da mutanen domin kamo su da ransu, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Yan daba sun dabawa wani dan kasuwa wuka a Kano

A wani labarin, wasu yan daba a kauyen Dakasoye da ke karamar hukumar Garun Malam ta jihar Kano sun caki wani dan kasuwa, Alhaji Auwalu Gambo, a safiyar ranar Litinin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Lamarin ya haddasa tsoro da juyayi a kauyen yayin da yan ta'addan suka je gidan marigayin sannan suka caccake shi sau da dama har sai da ya ce ga garinku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng