Yan Daba Sun Caki Wani Dan Kasuwa Har Lahira a Jihar Kano

Yan Daba Sun Caki Wani Dan Kasuwa Har Lahira a Jihar Kano

  • Yan daba sun halaka wani bawan Allah a kauyen Dakasoye da ke karamar hukumar Garun Malam ta jihar Kano
  • Maharan sun kashe Alhaji Auwalu Gambo wanda ya kasance dan kasuwa a gidansa ta hanyar caccakarsa da wuka
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin inda ta ce ta kaddamar da bincike a kai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wasu yan daba a kauyen Dakasoye da ke karamar hukumar Garun Malam ta jihar Kano sun caki wani dan kasuwa, Alhaji Auwalu Gambo, a safiyar ranar Litinin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Lamarin ya haddasa tsoro da juyayi a kauyen yayin da yan ta'addan suka je gidan marigayin sannan suka caccake shi sau da dama har sai da ya ce ga garinku.

Jami'an yan sanda
Yan Daba Sun Caki Wani Dan Kasuwa Har Lahira a Jihar Kano Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda abun ya faru, matar marigayin ta magantu

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

Da take zantawa da Freedom Radio, matar marigayin, Yahanaso Gambo, ta ce sun zo da misalin karfe 3:00 na tsakar dare suna bacci sannan suka tafi dakinsa kai tsaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce koda dai basu yi mata magana ba, sun daure mijin nata da igiya sannan suka fara dukansa wanda ya yi sanadiyar zubar da jininsa.

Ta ce:

"Sun tsallako ta katangar gidan makwabtanmu. Kusan su biyar ne. Muna bacci sannan suka bukaci mu tashi. Sai suka fara caccakar mijina da babbakla sassan jikinsa da dama. Basu daina ba har sai da ya mutu."

Da take magana, mahaifiyar marigayin, Hajiya Hamu Kabiru, wacce ke zaune da su a gidan ta ce:

"Bayan sun kashe shi sai suka bukaci na basu kudi; wanda na yi. Sun yi barazanar kashe ni idan ban koma dakina ba. Sun kashe shi yayin da muke kallo."

Kara karanta wannan

Kano: NLC Za Ta Shiga Takun Saka Da Abba Gida Gida Kan Albashin Ma’aikata Fiye Da 10,000

A halin da ake ciki, mazauna yankin sun koka kan hare-haren da yan daba ke kai masu, suna masu kira ga gwamnati da ta kawo masu agaji.

Wani mazaunin yankin, Aminu Muhammad Ilyas, ya ce:

"Muna fuskantar gagarumin matsala a yankin nan. Mutane na yawan zuwa imma don sace-sace ko kashe mutane. Muna so gwamnati ta taimaka mana sannan ta magance matsalar."

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullagi Haruna Kiyawa, ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

Sojoji sun kama barayin karafunan titin jirgi, sun ki amsar cin hancin miliyan N5

A wani labari na daban, dakarun rundunar sojojin Najeriya a Doma, jihar Nasarawa sun yi nasarar kama wasu masu sace karafunan titin jirgin kasa.

Har ila yau, sojojin sun ki amsar cin hancin naira miliyan biyar da wadanda ake zargin suka yi yunkurin basu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel