Masu Garkuwa Da Mutane Sun Tasa Keyar Mutum Hudu a Jihar Bauchi

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Tasa Keyar Mutum Hudu a Jihar Bauchi

  • Ayyukan masu garkuwa da mutane na ƙara ta'azzara a cikin ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da aƙalla mutum huɗu a yankin sannan suka buƙaci a biya kuɗin fansa
  • Miyagun kuma sun jikkata wani yaro tare da lalata babura da shagunan mutane a harin da suka riƙa kai wa a yankin

Jihar Bauchi - Wasu miyagu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne na ci gaba da cin karensu babu babbaka a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa aƙalla mutum huɗu masu garkuwa da mutanen suka sace yayin da suka raunata wani mutum ɗaya a yankin.

Masu garkuwa da mutane sun sace mutum hudu a Bauchi
Masu garkuwa da mutane na yawan kai hare-hare a Ningi Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Gamji inda suka yi awon gaban da wani ɗan kasuwa mai suna Daniel, sannan suka buƙaci a biya su kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Mutane da Yawa Sun Maƙale Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Rukunin Gidaje a Abuja

Ƴan bindigan dai sun kutsa cikin ƙauyen ne ranar Juma'a da misalin ƙarfe 8:40 na dare inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi domin korar mutane wanda hakan ya basu damar zuwa wajen Daniel, wani Inyamuri wanda ake tunanin cewa daman saboda shi suka shigo ƙauyen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A satin da ya wuce ƴan bindigan sun sace wani mutum mai suna Yahayya mai shekara 45 a duniya a ƙauyen Tabla inda suka buƙaci a biya N10m a matsayin kuɗin fansa kafin su sako shi.

Ƴan bindigan na yawan kai hare-hare a ƙauyuka

Haka kuma a Asabar ɗin da ta gabata, ƴan bindigan sun farmaki wasu ƙauyuka guda uku na Kuluki, Ruwan Dinya da Shande, inda suka tasa ƙeyar wani ɗan kasuwa mai suna Alh Muhammadu Kazami mai shekara 55 a duniya.

A ƙauyen Kuluki sun yi harbi kan mai uwa da wabi inda suka lalata babura masu yawa sannan suka fasa shagunan mutane.

Kara karanta wannan

Babban Jigo Ya Tona Asirin Manyan Sarakuna da Wasu Gwamnoni Masu Hannu a Talauta Arzikin Najeriya

Daga nan suka wuce zuwa Ruwan Dinya inda suka sace wani mai suna Bala El-B, da harbin wani yaro Abubakar Garba wanda yanzu haka ake duba lafiyarsa a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Birnin Kudu a jihar Jihawa.

'Yan Bindiga Sun Halaka Karamin Yaro a Bauchi

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai wani farmaki ana tsaka da cin kasuwa a jihar Bauchi inda suka salwantar da ran wani ƙaramin yaro mai shekara 13 a duniya.

Ƴan bindigan sun dai kai wannan farmakin ne a garin Jama'are inda suka yi awon gaba da wani hamshaƙin ɗan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel