Jigon APC: Gwamnoni da Wasu Sarakuna Na Da Hannu a Satar Ɗanyen Mai

Jigon APC: Gwamnoni da Wasu Sarakuna Na Da Hannu a Satar Ɗanyen Mai

  • Shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu (TSN) ya fallasa masu hannu a satar ɗanyen mai a Najeriya tun shekarar 1983
  • Kailani Muhammad ya ce ba sojijin ruwa da na ƙasa kaɗai ke da hannu ba harda wasu manyan Sarakuna da gwamnoni
  • Ya ce ya kamata shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tashi tsaye kuma ya shirya hukunta duk wanda aka gano yana da hannu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani babban jigon APC kuma shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu (TSN), Injiniya Kailani Muhammad, ya ce bayan sojojin Najeriya akwai wasu jiga-jigai da ke ɗaukar nauyin satar ɗanyen mai.

Jaridar Leadership ta rahoto jigon jam'iyya mai mulki na cewa wasu Sarakunan gargajiya da gwamnoni na da hannu a sace-sacen mai wanda ke neman talauta Najeriya.

Satar ɗanyen mai a Najeriya.
Jigon APC: Gwamnoni da Wasu Sarakuna Na Da Hannu a Satar Ɗanyen Mai Hoto: Leadership

Muhammad ya yi wannan furucin ne yayin da yake martani kan kalaman Asari Dakubo, wanda ya yi ikirarin cewa kaso 99 na ɓarayin mai sojin kasa da na ruwa ke ɗaukar nauyi.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

Ya ƙara da cewa wasu manyan Sarakuna da wasu gwamnoni a Najeriya suna da hannu a satar ɗanyen man biliyoyin daloli tsawon gomman shekaru tun shekarar 1983.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, Kailani Muhammad ya ce:

"Ba sojoji ne kaɗai ke da hannu a satar ɗanyen mai ba, wannan ɗanyen aiki ya haɗa da Sarakuna da wasu gwamnoni, duk suna da hannu kuma an fara ne tun a 1983. Mutane ne masu karfi sosai."
"Saboda haka dole shugaban kasa ya tashi tsaye, ya tsaya kan bakarsa kuma ya shirya hukunta duk wanda aka gano yana da hannu a gurgunta hanyar kuɗin shigarmu saboda shi ne tattalin arzikin kasar nan."
"Mun dogara ne da mai wajen tafiyar da ƙasar nan kuma babban abinda ya dace Tinubu ya yi shi ne kawo karshen satar mai saboda ya samu isassun kuɗin shigar da zai tabbatar da alkawarin da ya yi."

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sa Game Da Sabon Sufeto Janar Na 'Yan Sanda, Egbetokun Olukayode

Gwamna Aliyu Ya Kori Sakatarorin Ilimi Na Kananan Hukumomi 23 a Sakkwato

A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kori Sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar ta Arewa maso Yammacin Najeriya.

Gwamnan ya umarci baki ɗaya Sakatarorin da korar ta shafa su miƙa jagorancin hukumomin ilimin ga manyan ma'aikatan Ofis ɗinsu nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel