Har Yanzu Abdulrasheed Bawa Na Tsare a Hannun DSS Sati Daya Bayan Cafke Shi

Har Yanzu Abdulrasheed Bawa Na Tsare a Hannun DSS Sati Daya Bayan Cafke Shi

  • Abdulrasheed Bawa na ci gaba da kasancewa a tsare a hannun rundunar ƴan sandan farin kaya (DSS) sati ɗaya bayan kama shi
  • Rundunar ta DSS ta cafke Bawa ne bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi daga shugabancin hukumar EFCC
  • Daga manyan laifukan da Bawa ke amsa tambayoyi akai akwai rawar da ya taka wajen sauya fasalin ƙuɗaden ƙasar nan

Abuja - Dakataccen shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, na ci gaba da kasancewa a tsare a hannun rundunar ƴan sandan farin kaya, sati ɗaya bayan cafke shi, Daily Trust ta rahoto.

Duk da cewa jami'an hukumar basu bayyana laifukan da ake tuhumarsa da su ba, an fahimci cewa ana ci gaba da yi wa Bawa tambayoyi ne bisa rawar da ya taka wajen sauya fasalin kuɗi.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

Bawa na tsare a hannun DSS sati daya bayan kama shi
Dakataccen shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Wani majiya ya bayyana cewa akwai sauran wasu abubuwan da ake tatsar bayanai daga wajensa a kansu, amma dai rawar da ya taka a wajen sauya fasalin kuɗin ita ce akan gaba.

Jami'an rundunar ta DSS dai sun yi caraf da Bawa ne jim kaɗan bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ta kiraye-kirayen a saki Bawa

A halin da ake ciki ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana kuskuren DSS na ci gaba da tsare shi, inda suka yi kiran da ko dai a maka shi kotu ko kuma a sake shi ya shaƙi iskar ƴanci.

Wani ɗan rajin kare haƙƙin ɗan adam mai suna Salihu Aliyu, ya bayyana cewa:

"Yakamata DSS ta gaggauta bincikenta kan waɗannan mutanen, ina nufin Bawa da Godwin Emefiele, musamman na EFCC (Bawa) sannan ta tura su zuwa kotu. Ba mu san wane irin laifi ma ya aikata ba har yanzu!"

Kara karanta wannan

Tsohon Sufetan 'Yan Sanda, Usman Baba Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Korarsa Daga Aiki Da Shugaba Tinubu Ya Yi

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar DSS, Peter Afunanya, ya ci tura saboda ƙin ɗaga wayarsa da ya yi. Bai kuma dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba a wayarsa har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

DSS Ta Dira Gidan Abdulrasheed Bawa

Rahoto ya zo cewa rundunar ƴan sandan farin kaya ta da DSS na ci gaba da zurfafa binciken da ta ke yi akan dakataccen shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Jami'an rundunar sun dira gidan Bawa domin samo wasu hujjoji kan binciken da su ke yi a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel