Ciki Ya Ɗuri Ruwa, DSS Sun Je Gidan Abdulrasheed Bawa, An Zurfafa Binciken EFCC

Ciki Ya Ɗuri Ruwa, DSS Sun Je Gidan Abdulrasheed Bawa, An Zurfafa Binciken EFCC

  • Bayan an shiga ofishinsa da ke Hedikwatar EFCC a Jabi, Hukumar DSS ta shiga gidan Abdulrasheed Bawa
  • Jami’an tsaro sun lalube gidan Shugaban EFCC da aka dakatar da nufin samun hujjoji a binciken da ake yi
  • Bayan haka, DSS ta gayyaci wasu na-kusa da Bawa domin ayi masu tambayoyi game da zargin da ke wuyansu

Abuja - Dakarun hukumar DSS sun je gidan Abdulrasheed Bawa, inda su ka yi wani bincike na musamman bayan an dakatar da shi daga ofis.

Dazu aka samu rahoto daga Punch cewa jami’an tsaro masu fararen kaya na DSS sun laluba gidan Malam Abdulrasheed Bawa da ke garin Abuja.

Zuwa yanzu ba mu da masaniya game da makomar binciken da aka yi kan tsohon shugaban na hukumar EFCC da aka dakatar a makon jiya.

Kara karanta wannan

Tinubu: Tsare-Tsaren Sabon Shugaban Najeriya Na Daukar Idon Duniya – Birtaniya

Jami'an DSS
Jami'an DSS a Najeriya Hoto: Getty Images/Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya kai ga na kusa da Bawa

Haka zalika an gayyaci wasu daga cikin na-kusa da Bawa domin yi masu tambayoyi a kan zargin rawar da su ka taka wajen karkatar da dukiyoyi.

Ana zargin an yi awon gaba da dukiyoyin a aka samu bayan kotu ta karbe kadarori a hannun wasu da aka je kotu, aka mallakawa hukumar EFCC.

A ‘yan kwanakin nan aka taso na kusa da tsohon shugaban hukumar mai yaki da rashin gaskiya. Daily Trust ta ce an yi mako guda yana tsare.

Da Punch ta tuntubi Dr Peter Afunanya a matsayinsa na mai magana da yawun bakin hukumar DSS a Najeriya, sai ya nuna ba zai ce ko da uffan ba.

Gidan Mista Bawa ya na unguwar Gwarimpa a birnin tarayya, dakarun DSS sun auka ne domin yin bincike a gaban ‘ya ‘yansa da kuma mai dakinsa.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Maganar Farko Da Ya Shiga Hannun Hukumar EFCC

Wata majiya kuma ta ce a ranar Asabar da ta gabata, jami’an tsaron su ka shiga ofishin shugaban EFCC da ke Jabi, aka gudanar da wasu bincike.

Rahoton ya ce jami’an sun gabatar da takardar neman izini daga kotu kafin aukawa ofishin.

Wani jami’in gwamnati da ya yi magana a boye, ya ce zuwa DSS ba ta fara shirin kai karar tsohon shugaban EFCC kotu ba, ana kokarin tattara hujjoji.

Agbu Kefas ya kafa kwamiti

Makonni kadan da karbar mulki, sai ga labari cewa sabon Gwamnan Taraba ya cire sanayyar Jam’iyya, ya shirya yin bincike na musamman a jihar.

Sakataren gwamnatin Taraba, Gibeon-Timothy Kataps ya ce za a binciki abubuwan da su ka faru a duk ma'aikatu a lokacin mulkin Arc. Darius Ishaku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel