Shugaba Tinubu Ya Nada Sababbin Masu Bada Shawara 5 Daf da Zai Bar Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Nada Sababbin Masu Bada Shawara 5 Daf da Zai Bar Najeriya

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nada wasu karin mutanen da za su rika ba shi shawara a mulki
  • A cikin wadanda aka ba mukaman nan akwai Hadiza Bala Usman da Hannatu Musa Musawa
  • Bola Tinubu ya nada masu ba shi shawara a kan harkokin majalisa, sannan ya tabbatar da NSA

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin karin wasu da za su zama cikin masu ba shi shawara wajen gudanar da mulkinsa.

Labari ya zo daga The Cable cewa Mai girma shugaban kasa ya zabi Hadiza Bala Usman a matsayin mai bada shawara a wajen kula da tsare-tsare.

Hannatu Musa Musawa ta zama mai ba shugaban Najeriya shawara a harkar al’adu da nishadi.

Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mata 2 sun zama Hadimai

Kafin zaman ta mai bada shawara, Hadiza Bala Usman ta rike shugabancin hukumar NPA da shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnatin Kaduna.

Kara karanta wannan

Jirgin Bola Tinubu Ya Sauka a Faransa, An Ji Ranar da Shugaban Kasa Zai Dawo Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta fahimci Hannatu Musa Musawa ta na cikin wadanda su ka taka rawar gani wajen yakin neman zaben Bola Tinubu a APC mai-ci.

Mahaifinta, Musa Musawa kwararren ‘dan siyasa ne da aka yi a Katsina a lokacin tsohuwar Kaduna. Ita kuma Lauya ce da tayi karatu a gida da waje.

Masu bada shawara a Majalisa

Rahoton tashar Channels ya ce Sanata Abdullahi Abubakar Gumel ya zama babban mai bada shawara na musamman a kan harkar majalisar dattawa.

A gefe guda kuma tsohon ‘dan majalisa, Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim zai rika ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin majalisar wakilai.

Sauran mukamai da aka bada

Haka zalika Mallam Nuhu Ribadu ya samu karin matsayi daga mai bada shawara na musamman a kan tsaro zuwa NSA, ya shiga majalisar tsaro ta kasa.

Kara karanta wannan

Ribadu: Muhimman Abubuwa 7 Da Baku Sani Ba Game Da Sabon Mai Ba Da Shawara A Harkokin Tsaro

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce Adeniyi Bashir Adewale ya zama sabon shugaban kwastam, ya na mai canzar Kanal Hameed Ali.

Sababbin Hadiman shugaban kasa

1. Hadiza Bala Usman

2. Hannatu Musa Musawa

3. Sanata Abdullahi Abubakar Gumel

4. Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim

5. Mallam Nuhu Ribadu

Hafsoshin tsaro sun tafi

A jiya rahoto ya zo cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sababbin shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, an yi wa duka hafsoshin tsaro ritaya.

Bola Tinubu ya amince da naɗin CDS, COAS, IGP, NSA a yammacin Litinin 19 ga watan Yuni. Sanarwar ta fito ne a lokacin da yake shirin tafiya Faransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel