Babban Malamin Addinin Da Masu Garkuwa Da Mutane Suka Sace a Jihar Ondo Ya Kubuta
- Bayan kwashe kwana ɗaya a hannun masu garkuwa da mutane, babban malamin addinin musulunci a jihar Ondo ya kubuta
- Malam Ibrahim Oyinlade ya kuɓuta ne bayan ya yi kwana ɗaya a hannun masu garkuwa da mutanen sa suka sace shi
- Ƴan sanda sun tabbatar da sako malamin basu yi bayanin cewa ko an biya N10m kuɗin fansan da masu garkuwan suka buƙata ba
- Jihar Ondo - Babban malamin addini kuma limamin ƙauyen Uso a ƙaramar hukumar Owo ta jihar Ondo, Ibrahim Oyinlade, ya kuɓuta daga hannun waɗanda suka sace shi.
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa malamin mai shekara 67 a duniya, an sace shi ne a gonarsa da ke a sansanin Asolo a ranar Asabar da rana.
Wani ɗan'uwan malamin wanda baya son a ambaci sunansa ya tabbatar da cewa an sako malamin.
Majiyar ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan malamin a ranar Lahadi, inda suka buƙaci da a biya su kuɗin fansa har N10m.
"Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi ƴan uwansa a ranar Lahadi inda suka buƙaci a basu N10m amma mun godewa Allah an sako shi yanzi." A cewarsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ƙara da cewa ba zai iya tabbatar da cewa an biya kuɗin fansa ba ƙafin a sako Malam Oyinlade ba.
Ƴan sanda sun tabbatar da sako malamin addinin musuluncin
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da an sako malamin s ranar Litinin da safe, cewar rahoton Channels tv.
Ta bayyana cewa an sako malamin ne a daren ranar Lahadi amma bata bayar da bayani ba kan ko an biya kuɗin fansa kafin masu garkuwa da mutanen suka sace shi su sako shi ya shaƙi iskar ƴanci.
Jerin Mutum 12 Da Shugaba Tinubu Yakamata Ya Bincika Kan Wawure Dukiyar Kasa, Tsohon Dan Majalisa Ya Bayyana
Ɗaliban jami'ar UniJos Sun Kubuta
A wani labarin, ɗaliban jami'ar Unijos da ƴan bindiga suka dira har ɗakunan kwanansu suka ɗauke, sun kuɓuta daga hannun miyagun.
Ɗaliban guda shida ne dai daga cikin guda bakwai da ƴan bindigan suka yo awon gaba da su suka samu tsira daga hannun miyagun ƴan bindigan.
Asali: Legit.ng