Jihar Plateau: 6 Daga Cikin Daliban Unijos 7 Da Yan Bindiga Suka Sace Sun Kubuta

Jihar Plateau: 6 Daga Cikin Daliban Unijos 7 Da Yan Bindiga Suka Sace Sun Kubuta

  • Jami'an tsaro sun yi nasarar ceto mutane shida daga cikin bakwai da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Plateau
  • Har yanzu akwai sauran mutum daya tsare a hannun yan bindigar kuma yan sanda na kokarin ganin sun kubutar da shi
  • A ranar Laraba ne wasu miyagu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne suka farmaki dakunan kwanan daliban sannan suka yi awon gaba da su

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shida daga cikin daliban jami'ar Jos bakwai da aka yi garkuwa da su sun samu yanci bayan shafe kwanaki biyu a tsare.

An yi garkuwa da daliban wadanda ke zama a wajen makaranta a daren ranar Laraba a dakunansu da ke yankin Ring Road a karamar hukumar Jos ta arewa da ke jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

Taswirar jihar Plateau
Jihar Plateau: 6 Daga Cikin Daliban Unijos 7 Da Suka Sace Sun Kubuta Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Muna kokarin ceto mutum 1 da ya rage, kwamishinan yan sandan Filato

Kwamishinan yan sandan jihar wanda ya sanar da batun sakinsu a cikin wata sanarwa ya ce yan sanda na kokarin ceto mutum daya da ya rage a hannunsu, rahoton Peoples Gazatte.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta ce:

"A yau, rundunar yan sandan jihar Filato na fatan sanar da jama'a cewa biyar daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a ranar 13/06/2023 sun samu yancinsu.
"Rundunar ta shiga aiki nan take bayan ta samu rahoton sannan ta shiga aiki ba ji ba gani tare da hadin gwiwar sashin yaki da garkuwa da mutane, dangin wadanda aka sace da kuma al'ummar gari don ganin an sako mutanen.
"Daya daga cikin wadanda aka sacen ya yi nasarar tserewa daga sansanin masu garkuwa da mutanen, yayin da har yanzu daya ke tsare. Gaba daya mutanen da aka kubutar sun kama shida.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Mai Kudin Afrika, Aliko Dangote a Aso Rock

"Sai dai kuma, kwamishinan yan sandan Bartholomew N. Onyeka ya ba kwamandan yankin da DOP Nasarawa Gwong don tabbatar da ceto mutum na karshe ba tare da rauni ba da kuma kamo wadanda suka aikata ta'asar.
"Kwamishinan yan sandan ya sake ba mutanen jihar Plateau tabbacin cewa yana kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da kayayyaki a jihar. Saboda haka ya yi kira ga mazauna jihar da su kasance masu lura da tsaro, su kai rahoton ayyuka ko mutanen da basu yarda da su ba, sannan su ba da bayanai masu amfani da zai taimaka wajen yaki da laifuka a jihar."

Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban Unijos 7, sun nemi a biya kudin fansa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da ɗaliban jami'ar tarayya da ke Jos (UNIJOS) guda 7 ranar Talata da tsakar dare.

An tattaro cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na dare a daidai lokacin da ɗaliban suka tashi suna karatu domin jarabawar zango na biyu da suka fara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel