Magidanci Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotu a Jihar Kaduna Saboda Ta Ki Bar Masa Gida

Magidanci Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotu a Jihar Kaduna Saboda Ta Ki Bar Masa Gida

  • Wani magidanci ya garzaya wata kotun shari'ar musulunci a jihar Kaduna domin neman kotun ta raba shi da tsohuwar matarsa
  • Magidancin dai yana neman kotun ne da ta tilasta tsohuwar matarsa da ta bar masa gida saboda ya kammala datse igiyar aurensu
  • Ya yi ƙorafin cewa matar bata da tarbiyya domin har taron dangi ta taɓa gayyato ƴan uwanta sun lakaɗa masa dukan tsiya

Jihar Kaduna - Wani magidanci mai suna Mukhtar Ibrahim mai shekara 50 a duniya, ya garzaya wata kotun shari'ar musulunci mai zamanta a jihar Kaduna, inda ya maka tsohuwar matarsa ƙara.

Magidancin ya kai ƙarar tsohuwar matarsa gaban kotun ne inda yake neman kotun da ta sanyata ta bar masa gidansa, a cewar rahoton Tribune.

Magidanci ya kai karar tsohuwar matarsa kotu
Magidancin ya koka kan ta ki bar masa gida Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Mai shigar da ƙarar wanda ya shigar da kokensa ta hannun lauyansa Jamilu Sulaiman, ya kuma buƙaci kotun ta tabbatar da saki na ukun da ya yi wa wacce yake ƙara.

Kara karanta wannan

"Gida Najeriya Zan Dawo": Kyakkyawar Budurwa Mai Rayuwa a Kasar Waje Ta Koka Kan Rashin Samun Saurayi, Bidiyonta Ya Yadu

Magidancin ya koka cewa rayuwarsa na cikin hatsari

Ya bayyana cewa rayuwarsa na fuskantar barazana saboda ci gaba da zaman da ta ke yi a gidan nasa, wanda hakan ya hana shi samun sukuni kwata-kwata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Ina son a bani ikon ci gaba da riƙe ƴaƴana saboda bata da tarbiyya. Ta taɓa kiran ƴan uwanta suka lakaɗa min duka, inda suka barni da raunika da tabbai."
"A yanzu haka, rayuwata cikin fargaba ta ke na kasa samun sukuni tun da ta ƙi yarda ta bar min gida."
Wacce ake ƙarar bata samu halartar zaman kotun ba amma masinjan kotun ya tabbatar da cewa ya bata sammaci.

Alƙalin kotun, mai shari'a Malam Isiyaku Abdulrahman, ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 10, ga watan Yulin 2023.

Miji Ya Nemi Saki a Kotu Kan Kara Auran Da Matarsa Ta Yi

Kara karanta wannan

Likita Ya Faɗa Wa Wani Mutumi Kar Ya Kusanci Matarsa Saboda Abu 1, Da Suka Koma Gida Ya Ba Da Mamaki a Bidiyo

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan kasuwa ya garzaya kotu neman a ɗatse igiyar aurensa da matarsa saboda ta fita waje ta ƙara yin wani auren bada saninsa ba.

Magidancin ya bayyana cewa matar tasa ta sulale ta bar gidansa inda ta ƙara wani auren a sirrance duk da akwai aurensa a kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel