"Gida Najeriya Zan Dawo": Kyakkyawar Budurwa Mai Rayuwa a Kasar Waje Ta Koka Kan Rashin Samun Saurayi

"Gida Najeriya Zan Dawo": Kyakkyawar Budurwa Mai Rayuwa a Kasar Waje Ta Koka Kan Rashin Samun Saurayi

  • Wata budurwa mai rayuwa a ƙasar waje ta nuna takaicinta kan yadda duk kwalliyar da za ta yi ta fito, babu namijin da yake tanka mata
  • Ta bayyana ko mutum ɗaya bai taɓa tsayar da ita da sunan ya rage mata hanya a motarsa ba ko ya yi mata magana akan hanya
  • A dalilin rashin masu tayawa, budurwar ta bayyana cewa ta fara shirin dawowa gida Najeriya, inda maza za su riƙa kulata

Wata budurwa ƴar Najeriya mai rayuwa a ƙasar waje, tana cikin baƙin ciki kan cewa ba namijin da yake yabawa da tsabagen kyawun da ta ke da shi.

Kyakkyawar budurwar a cikin wani bidiyo ta bayyana cewa ta ci kwalliya ta fito, amma babu namijin da ya tareta ya gaya mata cewa ta yi kyau sosai.

Kara karanta wannan

"Na Gaji Da Zama Babu Aure": Shahararriyar 'Ƴar TikTok Ummi Darling Na Neman Mijin Aure

Budurwa ta koka kan rashin samun mashinshini a kasar waje
Budurwar tace duk da.kyawunta babu mai kulata Hoto: @Instablog9ja
Asali: Twitter

Haka kuma, tace duk da kwalliyar da ta sha da kyawunta, babu mai motar da ta tsaya domin ya tambayi ko hanya ɗaya suka yi ya rage mata hanya.

Ta shiga cikin takaici da mamaki a lokaci ɗaya, saboda da ace a nan gida Najeriya ne to da ba wannan labarin ake ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurwar ta bayyana cewa gida Najeriya za ta dawo saboda ƙarancin mashinshina da ta ke fama da su a inda ta ke rayuwa.

Shafin @Instablog9ja shi ne ya sanya bidiyon a manhajar Twitter.

Ƴan soshiyal midiya sun yi tsokaci

@EgwuSamuel49 ya rubuta:

"Gwara ki tsaya a inda kike. An cire tallafin man fetur...Babu mai zuwa inda wani yake yanzu."

@brickzofficial ya rubuta:

"Nan bada daɗewa ba ƴan matan da kansu za su fara neman aurenmu da biyan kuɗin sadaki."

Kara karanta wannan

"Sai Da Ya Yi Hawaye": Matashiya Ta Ba Direba Mai Kirki N10,000 Bayan Ya Caje Ta N2,500 Duk Da Tsadar Mai

Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta Ya Tsere

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koka bayan saurayin da su ke kwasar soyayya tare ya tsere ya bar ta, wanda hakan ya dame ta.

Budurwar ta bayyana cewa saurayin na ta gaba ɗaya yi bulokin ɗinta ta yadda ba za ta iya tuntuɓarsa ba ta ko ina wanda hakan yana mata tuwo a ƙwarya.

Budurwar ta bayyana cewa saurayin na ta ya ɗauki wannan matakin ne bayan ta yi masa wani abinci ya ɗanɗana ya ji irinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel