Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa

Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa

  • Wani mutumi ya shiga ƙunci bayan Likita ya shawarce shi da matarsa kar su kusanci juna na tsawon kwanaki 7 watau mako ɗaya
  • Bayan kammala yi wa ma'auratan tsarin taƙaita iyali, Likita ya faɗa musu su ɗan yi hakuri da juna na tsawon mako guda
  • Sai dai mutumin bai ji daɗin wannan shawara ba domin ganinsa wannan jiran bai zama wajibi ba tunda dai an yi musu tsarin iyali

Wani magidanci ya shiga yanayin damuwa sakamakon abinda Likita ya gaya masa shi da matarsa cewa su jira tsawon mako ɗaya gabanin su kusanci juna.

Bayan an musu tsarin taƙaita iyali shi da matarsa, kwararren likitan ya shawarci mutumin ya haƙura na ɗan wani lokacin kafin ya kwanta da matarsa.

Yadda ta kaya tsakanin ma'aurata.
Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa Hoto: @itzz_joygray
Asali: TikTok

Sai dai ga dukkan alamun da suka bayyana karara a fuskar magidancin bai ji daɗin shawarar da Likitan ya basu ba, ya faɗa wa matar cewa su shure zancen domin ba bukatar su jira.

Kara karanta wannan

"Gida Najeriya Zan Dawo": Kyakkyawar Budurwa Mai Rayuwa a Kasar Waje Ta Koka Kan Rashin Samun Saurayi, Bidiyonta Ya Yadu

Lokacin da suka bar wurin likita suka koma gida, matar ta tambayi sahibin nata meyasa ya ɓata ransa, kuma nan take ya yi fatali da shawarar likitan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matar ta ci gaba da rarrashinsa tana masa kalamai nasu daɗi kan ya yi haƙuri. Shafin @itzz_joygray ne ya wallafa bidiyon yadda ta kaya tsakanin ma'auratan.

Yayin wallafa a Bidiyon a TikTok, ta rubuta cewa:

"Mun yi tsarin iyali, Likita ya ce mu ɗan jira na tsawon mako ɗaya kafin wani abu ya shiga tsakaninmu."

Kallo bidiyon abinda ya faru a nan

Martanin wasu mutane kan bidiyon

Bayan kallon bidiyon ma'auratan, da yawan masu amfani da soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakinsu, wasu kuma sun faɗi abinda ya faru tsakaninsu da abokan zamansu.

@Blossom ta ce:

"Idan da zan ce wa mai gidana ya taya ni wanke-wanke, cewa zai yi sai na ba shi wani abu. Wanda bai iya hakura da wannan ba ina ga an je babban lamari."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

@Charlene Temitope ta ce:

"Ah to me zamu jira."

@_mercified_01 ta ce:

"Haka mijina yake, ni fa wannan abun ma zafi yake mun."

Matashi Mai Samun N100k Ya Bukaci Budurwa Mai Samun N34m Ta Aje Aikinta Ta Aure Shi

A wani labarin na daban kuma wani matashin Saurayi ya je wurin budurwarsa da ya ke son ya aura da wata buƙata mai ban mamaki da jan hankali.

Mutane da dama sun caccaki wani matashi ɗan Najeriya a yanar gizo, bayan ya buƙaci budurwarsa da ta ajiye aikin da ta ke yi saboda shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel