“Ku Binciki Kanku”: Matashi Ya Hana Mutane Fita Daga Jirgi Saboda Ya Nemi Kilishinsa Ya Rasa

“Ku Binciki Kanku”: Matashi Ya Hana Mutane Fita Daga Jirgi Saboda Ya Nemi Kilishinsa Ya Rasa

  • An sha yar dirama a cikin wani jirgin sama yayin da wani fasinja ya tsare mutane bayan ya nemi kilishinsa ya rasa
  • Mutumin wanda ya fusata ya yi ihu da babban murya sannan ya hana fasinjoji sauka daga jirgin
  • Ya kai ga har ya yi zazzafan musayar yawu da wani fasinja namiji wanda ya caccaki yadda ya dunga bi yana dube-dube

Wani matashi dan Najeriya ya yi yar karamar hauka bayan ya isa inda zai sauka amma sai ya nemi jakar kilishinsa ya rasa.

Mutumin wanda ya fusata ya hana wasu fasinjoji sauka daga jirgin yayin da ya nemi a dawo masa da jakar kilishinsa da ta bata.

Fasinjoji a jirgin sama da kilishi
“Ku Binciki Kanku”: Matashi Ya Hana Mutane Fita Daga Jirgi Saboda Ya Nemi Kilishinsa Ya Rasa Hoto: @whiteshark_blog
Asali: TikTok

Wannan abu da ya yi ya haddasa yar dirama a cikin jirgin saman yayin da mutane suka yi kokarin fahimtar abun da ke faruwa.

Kara karanta wannan

"Na Koyi Darasi": Matashi Ya Ajiye Aikinsa Mai Gwabi Domin Ya Kasance Da Budurwarsa, Sun Rabu Bayan Sati 2

A lokacin da wani mutum ya kalubalanci abun da ya aikata, sai mai kilishin ya amsa masa da harshen yarbancio, inda ya yi amfani da zafafan kalamai. Ya koka cewa ya duba jakar amma bai gani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Diramar wacce aka nada a bidiyo ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Pastor Pam Gabriel ya ce:

"Dole ka koyi darasi."

Angel ta ce:

"Kilishi na da tsada ban ga laifinsa ba."

Mame ta ce:

"Allah kadai ya san abun da ya nannade a cikin wannan kilishin."

Monalisa ta ce:

"Don Allah ka caje kowa faaa kilishi da ke da tsada haka."

queenethbob826 ta ce:

"Ina gani ba ni kadai bace ke matukar son kilishi."

Viv ta ce:

"Kowa da kowa oooo, ku binciki kanku, ku binciki kanku sannan ku binciki kanku."

Kara karanta wannan

"Sai Da Ya Yi Hawaye": Matashiya Ta Ba Direba Mai Kirki N10,000 Bayan Ya Caje Ta N2,500 Duk Da Tsadar Mai

Brown sugar XoXo ya ce:

"Kowa da kowa, ku binciki kanku, ku binciki kanku sannan ku binciki kanku."

Matashi ya yi wuff da sahibarsa baturiya, ta yi kaka da shi

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce bayan ya angwance da sahibarsa baturiya wacce ta isa yin kaka da shi.

Da yake fallasa sirrin zuciyarsa, matashin ya bayyana cewa ba zai iya rayuwa babu amaryar tasa ba. Wasu na ganin ba saboda Allah ya yi auren ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel