Cikar Ajali: Wani Matashi Mahayin Doki Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Dattijo Mai Shekaru 70 a Duniya
- Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar dattijon da wani mahayin doki ya buge a karamar hukumar Ringim
- Mahayin dokin mai suna Muhammad Mustapha mai shekaru 25 ya buge dattijon ne mai shekaru 70 akan kekensa a unguwar Maina
- Jami'an 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar dattijon a babban asibitin Ringim tare da tsare mahayin dokin a ofishinsu
Jihar Jigawa - Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani dattijo dan shekara 70 bayan wani mahayin doki ya buge shi.
A ranar Asabar ne 10 ga watan Yuni wani matashi mahayin dokin ya buge dattijon a unguwar Maina cikin karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa.

Source: Facebook
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Lawal Jiisu ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni na wannan shekara.

Kara karanta wannan
“Guba Wani Ya Saka Musu A Abinci” An Tsinci Gawar Mata Da Miji Kwance Cikin Gidansu A Abuja
Mahayin ya gagara shawo kan dokin tare da buge dattijon
Ya ce a ranar Asabar 10 ga watan Yuni, wani mahayin doki mai suna Muhammad Mustapha mai shekaru 25 ya gagara shawo kan dokin da yake kai tare da buge wani dattijo mai keke a cikin unguwar Maina.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dattijon mai shekaru 70 mai suna Umar Hassan da ke unguwar Galadanci an buge shi ne akan kekensa inda ya samu raunuka da dama da kuma karaya a kafarsa ta hagu da kuma kafadarsa.
Ya kara da cewa jami'an 'yan sandan sun isa wurin da abin ya faru tare da daukan marar lafiyar zuwa babban asibitin Ringim, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.
'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar dattijon a asibiti
Jiisu ya tabbatar da cewa dattijon daga baya ya rasa rayuwarsa a asibitin bayan an fara ba shi kulawa na musamman.

Kara karanta wannan
Nasara Daga Allah: Rundunar Sojin Najeriya Ta Cafke Matasa ’Yan Kungiyar 'Marlians' 15 a Jihar Arewa
Ripples Nigeria ta tattaro cewa, jami'an 'yan sandan sun mika gawar mamacin ga 'yan uwansa don shirye-shiryen binnewa yayin da hukumar ke ci gaba da tsare mahayin dokin.
Yan Sanda Sun Damke Wasu Masoya Kan Binne Jaririn Da Suka Haifa Da Ransa A Jigawa
A wani labarin, Rundunar 'yan sanda sun cafke wasu mutane biyu bisa zargin binne jariri da ransa a jihar Jigawa.
Wadanda ake zargin, Balaraba Shehu da saurayinta Ahmadu Shehu ana zargin sun haifi yaran ne ba ta hanyar aure da kuma binne shi da ransa.
Asali: Legit.ng