Yan Sanda Sun Damke Wasu Masoya Kan Binne Dan Gaba Da Fatiha Da Suka Haifa Da Ransa A Jigawa

Yan Sanda Sun Damke Wasu Masoya Kan Binne Dan Gaba Da Fatiha Da Suka Haifa Da Ransa A Jigawa

  • Yan sanda sun kama Balaraba Shehu da saurayinta mai suna Ahmadu Sale a kauyen Tsurma, karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa
  • Masoyan sun hada baki wajen binne jinjirin da suka haifa ba ta hanyar aure ba jim kadan bayan haihuwarsa kuma da ransa
  • Jami'an tsaro sun zakulo yaron daga cikin ramin amma tuni rai yayi halinsa kamar yadda likita ya tabbatar

Jigawa - Jami'an yan sanda a jihar Jigawa sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da saurayinta, Ahmadu Sale kan binne jinjirin da suka haifa da ransa a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce bayan Balaraba ta haihu ba ta hanyar aure ba sai ta hada kai da Amadu wajen aikata laifin, rahoton Vanguard.

Jami'an yan sanda
Yan Sanda Sun Damke Wasu Masoya Kan Binne Dan Gaba Da Fatiha Da Suka Haifa Da Ransa A Jigawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tono jinjirin amma ya ce ga garinku

DSP Shiisu ya ce an tono jinjirin daga ramin da mahaifiyarsa ta tona ta binne shi a kusa da masan gidansu, rahoton Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"A ranar 2 ga watan Disamban 2022, da misalin karfe 2350hrs, rundunar rahoto da ke bayyana cewa wata mata mai suna Balaraba Shehu mai shekaru 30, a kauyen Tsurma, karamar hukumar Kiyawa ta haihu sannan ta binne jinjirin.
"Da samun rahoton, sai aka tura wata tawagar jami'an yan sanda zuwa wajen da aka aikata laifin.
"Da isarsu wajen, sai jami'an tsaron suka shiga aiki sannan suka zakulo jinjirin daga cikin ramin da mahaifiyarsa ta tona kusa da bandakin gidansu sannan ta binne shi a ciki. An gaggauta kai yaron babban asibitin Dutse kuma wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.
"An kama wacce ake zargin kuma a yanzu haka tana tsare a hannun yan sanda.

"Binciken da ake gudanarwa ya kai ga kama wani Amadu Sale da aka fi san da Dan Kwairo mai shekaru 25 na kauyen Akar da ke karamar hukumar Kiyawa.
"Amadu ne ake zargin ya yi ma Balaraba ciki ba ta hanyar aure ba kuma da shi aka hada kai don binne jinjirin bayan an haife shi."

DSP Shiisu ya kara da cewa:

"Za a kwashi masu laifin zuwa kotu don fuskantar hukunci da zaran an kammala bincike."

Yan bindiga sun sace basaraken Ondo, sun bukaci a biya miliyan N100

A wani labari na daban, maharan da suka yi garkuwa da wani basaraken kasar Yarbawa sun bukaci a biya makudan kudade kafin su sako shi.

Yan bindigar sun bukaci yan uwan Oloso na Oso-Ajowa Akoko, Oba Clement Olukotun, da su biya naira miliyan 100 na fansarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel