Tsadar Mai: Makarantun Firamare da Kananan Sakandare a Edo Za Su Koma Karatun Kwanaki 3

Tsadar Mai: Makarantun Firamare da Kananan Sakandare a Edo Za Su Koma Karatun Kwanaki 3

  • Yayin da tsadar man fetur ke kara jawo matsala a Najeriya, gwamnatin Edo ta samo mafita ga fannin ilimi a firamare da karamar sakandare
  • Yanzu haka, za a fara karatun kwanaki uku a mako a madadin biyar da aka saba dashi a cikin makon karatu
  • Hakazalika, ma'aikatan gwamnati za su fara batun rage kwanakin aiki don rage radadin tafiyar da aiki a jihar

Jihar Edo - Gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa makarantun firamare da kananan sakandare a jihar za su fara karatun kwanaki uku kacal a mako farawa daga ranar 13 ga watan Yuni.

Shugabar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Edo (SUBEB) Misis Ozavize Salami ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Benin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

Ta fadi hakan ne bayan wata ganawa da shugaban ma’aikata da sauran jami’an gwamnatin jihar suka yi kan yunkurin gwamnati na mayar da kwanakin karatu zuwa kwanaki uku a mako.

An mayar da kwanakin karatu zuwa 3 a mako a Edo
Yayin tattaunawa kan makomar karatu a Edo | Hoto: tribuneonlineng.net
Asali: UGC

Yadda gwamnati ta tsara tafiyar da makarantu a Edo

Salami ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An zabi ranakun Litinin, Talata da Laraba a matsayin ranakun da yaranmu za su je makaranta yayin da za a rufe makarantu a ranakun Alhamis da Juma’a.
“Tsarinmu na wannan lokacin ya mayar da hankali ne kan habaka karatu ta yanar gizo don tabbatar da cewa yaran sun kammala tsarin darussan da ya kamata su dauka.
"Za su zauna a haka na tsawon makwanni shida kafin hutu. Bisa la'akari da dalilai na gudanarwa, mun zabi kwanaki uku na farkon mako domin dalibai su zo makaranta.
“Mun kara sa’o’in karatun firamare a fadin jihar da sa’a daya sai kuma sa’o’i biyu ga kananan makarantun sakandare domin cimma tsarin darussan tare da sanya jadawalin ranakun Alhamis da Juma’a zuwa ranakun Litinin, Talata da Laraba.”

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Za a rage kwanakin zuwa aiki a jihar Edo

Shima da yake nasa jawabi, shugaban ma’aikatan jihar Anthony Okungbowa, ya ce rage kwanakin aiki na ofis ba zai shafi tasirin aiki da ingancinsa ba, Tribune Online ta ruwaito.

Ya umarci shugabannin hukumomi da sakatarorin dindindin na ma’aikatu daban-daban da su samar da tsarin aiki tare da tabbatar da ba a samu matsalar gibi a aikinsu ba.

Ya ce gwamnati za ta samar da motocin bas da za su yi jigila tsakanin gidan gwamnati, sakateriyar jiha da sauransu don taimakawa wajen rage radadin tsadar mai ga ma’aikata a jihar.

Ya kara da cewa gwamnati ta gano hanyoyi takwas a cikin birnin, inda za ta samar da motocin bas din don rage radarin farashin sufurin mazauna birnin.

Kungiya ta bayyana yiwuwar fadawa yajin aiki da zanga-zanga

A wani labarin, kungiyar kwadago ta ce za ta yi zanga-zanga idan ba a yi waje da batun janye tallafin man fetur ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka Bayan Janye Tallafin Fetur

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta bayyana janye tallafin mai don habaka tattalin arzikin kasa.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da sharhi da cece-kuce kan lamarin, 'yan Najeriya na ci gaba da jure takaicin tsadar man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel