Dan Banga Ya Bindige Wani Mutum Saboda Zargin Kwace Masa Budurwa Da Ya Yi

Dan Banga Ya Bindige Wani Mutum Saboda Zargin Kwace Masa Budurwa Da Ya Yi

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas na gudanar da bincike kan lamarin da wani ɗan banga ya bindige wani mutum har lahira saboda ya yi wa budurwarsa magana
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nnwonyi Emeka ya gargaɗi 'yan bangan kan wuce gona da iri da suke yi da kuma take haƙƙin bil’adama da wata kungiyar 'yan bangan ke yi
  • Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Victor Erivwede, ya bayyana cewa ‘yan kungiyar banga ta OSPAC, na da hannu wajen aikata miyagun laifuka da dama a jihar

Rivers, Port HarCourt - Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta ce tana gudanar da bincike kan wani lamari da wani ɗan banga ya bindige wani mutum saboda zargin kula budurwarsa da yake yi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nwonyi Emeka, a zantawarsa da manema labarai a Fatakwal, ya yi gargadi kan yawaitar ‘yan banga a jihar, saboda mafi yawa daga yan bangan wata ƙungiyar banga OSPAC, duk masu laifi ne a wurin jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Taimaki APC Wajen Raba Kan ‘Yan Adawa a Zaben Majalisa

'Yan banga na aikata laifuka da dama a jihar Ribas
An tuhumi dan banga da halaka wani mutumi a kan budurwa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Yan banga sun koma aikata laifuka bayan ta'ammali da 'yan siyasa

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan, Victor Erivwede, wanda shi ne mai kula da sashen binciken manyan laifuka da leƙen asiri na jihar, SCIID, ya ce ana yawan samun laifin cin zarafin bil’adama da kungiyar ‘yan bangan ke yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce da farko 'yan bangan na OSPAC suna yin abin da ya kamata, amma daga lokacin da suka fara karbar aikin 'yan siyasa, sai suka bauɗe suka kama aikata laifuka, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Victor ya ƙara da cewa, da ace yana da iko, da lallai zai bai wa kwamishina shawarar a ƙara duba yanayin yadda suke gudanar da aiki.

Ana yawan kawo ƙarar 'yan banga a Ribas

Ya ce mafi yawansu ana yawan kawo ƙararsu kan yawan samunsu da ake yi da aikata miyagun laifuka.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Waiwayo Kan Masu Kwasar Ganima, Kusan Mutum 50 Sun Shiga Gagarumar Matsala a Kano

A cewarsa:

“Yawancin 'yan OSPAC masu laifi ne. Ina da wata shari’a a gabana, inda wani dan banga ya harbe wani mutum har lahira saboda wai ya yi magana da budurwarsa.”

A nasa bangaren, kwamishinan 'yan sandan jihar ta Ribas, Emeka, ya ce duk da cewa 'yan bangan suna da amfani, hakan ba yana nufin za su zura musu ido suna cin karensu babu babbaka ba.

Kwamishinan ya ce:

"Ba za mu yarda da yanke hukunci da ka da 'yan bangan je yi ba. Ba za ta yiwu ace masu kare rayuka da dukiyoyin jama'a, su ne kuma ke bi suna kashe mutane. Dole ne mu daƙile wannan zaluncin da ’yan bangan ke yi.”

Kwamishina ya ce 'yan bangan ba su da hurumin yanke hukunci

Ya kuma bayyana cewa, 'yan bangan ba jami'an tsaro ba ne, inda ya ce an taɓa samun lokacin da suka koma masu karɓowa mutane basussuka, wanda suka riƙa gallazawa mutane a dalilin hakan.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutum 2 a Birnin Tarayya Abuja

Kwamishinan ya ƙara da cewa aikin 'yan bangan shi ne su kama wanda ake tuhuma da laifi da kuma musayar bayanai tsakaninsu da jami'an tsaro.

Da yake zantawa da shugabannin 'yan banga na jihar, kwamishinan ya ce:

“Ba ku da ikon tsarewa ko yin bincike. Idan kotu ta yankewa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai aka samu wani ya harbe shi, to wannan da ya yi harbin ya aikata laifin kisa.”

Jaridar The Punch ta kawo wani rahoto a kwanakin baya, inda ake zargin 'yan bangan na OSPAC, da laifin kashe wani tsohon shugaban wani ƙauye da ke jihar rlta Ribas, mai suna Okechukwu Eleonu.

Budurwa mai samun sama da naira miliyan 3 ta bayyana irin mijin da za ta aura

A wani labarin na daban, Legit.ng ta kawo muku labarin wata matashiya mai samun N3.7m a duk wata da ta bayyana irin mijin da take so ta aura.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Wa APC Wankin Babban Bargo a Kaduna, Ya Bayyana Wani Bangare Na Musamman Da Jami'yyar Ta Gaza

Ta wallafa rubutun neman mijin auren ne a wani shafin haɗin aure na Tuwita, wanda ya janyo zazzafar muhawara a tsakanin masu amfani da kafar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel