Abba Gida-Gida Ya Waiwayi Barayin Kayan Rusau, An Kama Mutum 49

Abba Gida-Gida Ya Waiwayi Barayin Kayan Rusau, An Kama Mutum 49

  • Jami'an yan sanda sun yi ram da wasu da ake zaton yan daba ne masu satar kayan shaguna da sunan ganima
  • Matasa a Kano na fakewa da aikin rusau na gwamnatin Abba Gida-Gida, su sace kayan jama'a masu daraja
  • Mai magana da yawun yan sanda, SP Kiyawa, ya ce sun kama kusan mutum 50 a yankin karamar hukumar Fagge, cikin garin Kano

Kano - Hukumar 'yan sandan Kano ta tabbatar da damƙe mutane 49 da ake zargin suna da hannu dumu-dumu a satar kayayyaki a rukunin shagunan Triumph Plaza, ƙaramar hukumar Fagge.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin Tuwita.

Barayi.
Abba Gida-Gida Ya Waiwayi Barayin Kayan Rusau, An Kama Mutum 49 Hoto: @KanoPoliceNG
Asali: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun samu wannan nasara ne yayin da sabon gwamnan Kano, Abbba Kabir Yusuf, ke ci gaba da aikin rusau a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Tsoffin Gwamnoni 3 Na APC da PDP, Bayanai Sun Fito

Bisa haka matasa suka rika fakewa da rusau na gwamnati Abba, watau Abba Gida-Gida, suka riƙa zuwa suna ɗibar abinda suke kira da ganima a baraguzan ginin da aka rushe da wasu wuraren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan sanda suka fara cafke masu ɗibar ganima

Da yake tabbatar da kamen mutanen, SP Kiyawa ya ce:

"Ranar 4 ga watan Yuni, mun samu rahoto daga cikakkun yan ƙasa masu kishi cewa wasu 'yan zauna gari banza sun fara shirye-shirye da kulle-kullen yadda zasu je su kwashi ganima a shagunan Triumph Plaza, Fagge LG, Kano."
"Bayan samun rahoton, nan take kwamishinan yan sanda, Mohammed Gumel, ya umarci a tura jami'ai wurin su tabbatar da zaman lafiya kuma daga isarsu Plazan suka kama waɗanda ake zargi."
"Mutum 49 sun shiga hannu, kuma jami'an sun kwato kayayyakin da suka sace kamar Ƙofofi, tagogi da na'urar sanyaya yanayi (AC) da sauran muhimman kaya."

Kara karanta wannan

Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

Bayan haka ne kakakin yan sandan ya buƙaci iyaye da masu rike 'ya'ya su ja kunnen yaransu, karsu yarda su shiga cikin masu sace dukiyar mutane.

Kotu Ta Dakatar da NLC da Wasu Kungiyoyi Daga Shiga Yajin Aiki

A wani labarin na daban kun ji cewa an gamu da cikas, kotu ta hana NLC da wasu kungiyoyi shiga yajin aiki kan cire tallafin Mai.

Kotun ɗa'ar ma'aikata mai zama a Abuja ta dakatar da shirin tsunduma yajin aiki wanda ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ke yi kan cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel