Tsohon Gwamnan PDP Ya Taimaki APC Wajen Raba Kan ‘Yan Adawa a Zaben Majalisa

Tsohon Gwamnan PDP Ya Taimaki APC Wajen Raba Kan ‘Yan Adawa a Zaben Majalisa

  • Jam’iyyar APC ba ta da rinjayen da za ta iya kafa shugabancin majalisa ba da taimakon ‘yan adawa ba
  • Daga cikin ‘yan jam’iyyun hamayyan da ke taimakawa APC a majalisar tarayya akwai Nyesom Wike
  • Mutanen Wike sun sabawa ‘yan PDP da ke takama da yawan ‘yan adawa, sun bi Hon. Tajuddeen Abbas

Rivers - A zaben shugaban kasa da aka yi a 2023, Nyesom Wike ya mara baya ne ga Bola Ahmed Tinubu, a maimakon jam’iyyarsa ta PDP mai adawa.

Wani dogon rahoto da Premium Times ta fitar, ya nuna har yanzu akwai alaka mai kyau tsakanin tsohon Gwamnan na Ribas da sabon shugaban Najeriya.

A yayin da Hon. Idris Wase ya ziyarci Nyesom Wike a kan batun shugabancin majalisa, ‘dan siyasar ya nuna masa yana tare da wanda APC ta tsaida.

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

Tsohon Gwamnan Ribas
Bola Tinubu da Nyesom Wike Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Jim kadan bayan an yi haka sai aka ji Kingsley Chinda wanda mutumin Wike ne, sun kafa wani kwamiti da yake tallata Tajuddeen Abbas a majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya kai ‘dan majalisar na Ribas ya hada-kai da Femi Gbajabiamila bayan shugaban majalisar ne ya yi masa kafa, ya hana shi mukami a 2019.

Chinda ya zama mutumin Gbaja

Rahoton ya tuna yadda shekaru hudu da suka wuce, Gbajabiamila ya yi sanadiyyar zaman Ndudi Elumelu shugaban marasa rinjaye a maimakon Chinda.

A yau dangantakar da ke tsakanin ‘yan majalisar ta yi kyawun da har Gbajabiamila ya kafa wasu kwamitoci hudu, kuma ya ba Chinda rikon wata kujera.

Wike ya kawo sabani

‘Dan majalisar PDP, Fred Agbedi da wasu mutanensa su na kokarin hana APC samun shugabancin majalisa domin ganin yawan kujerun jam’iyyun hamayya.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

Ana haka sai aka ji Wike ya raba kan ‘yan adawa, ya jawo masu ‘yan taware a cikin tafiyarsu ta hanyar fito da Idu Igariwe wanda yake goyon bayan Abbas.

Za a murkushe ‘yan adawa

Rabiu Kwankwaso ya zauna da Bola Tinubu kwanaki a Faransa, kuma a halin yanzu manyan zababbun ‘yan jam’iyyar NNPP a majalisa su na tare da APC.

Jam’iyyar ADC wanda ta ke karkashin jagorancin Leke Abejide a majalisa, ta na goyon bayan Abbas da Benjamin Kalu, hakan ba zai yi wa PDP dadi ba.

Atiku v Keyamo a Kotu

Yanzu labari ya zo mana cewa tsohon Ministan kwadago, Festus Keyamo, zai lalo kudi ya biya ‘Dan takaran PDP a zaben 2023 watau Atiku Abubakar.

Festus Keyamo ya kai Atiku Abubakar, ya ce dole a binciki zargin rashin gaskiya da ake yi masa, a karshe kotu ta zartar da hukuncin da bai masa dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel