Budurwa Mai Samun N3.7m a Wata Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke Son Yin Wuff Da Shi

Budurwa Mai Samun N3.7m a Wata Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke Son Yin Wuff Da Shi

  • Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya mai neman mijin aure, ta bayyana irin namijin da ta ke son samu a matsayin miji
  • A cikin rubutun da ta yi a Twitter, ta bayyana cewa tana son samun namiji wanda aƙalla ya ke samun N3m a wata, sannan dole ya kasance mutum mai kirki
  • Budurwar ta kuma bayyana cewa aikin da ta ke yi na injiniyan software, tana samun N3.7m da shi a kowane wata

Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya, mai neman mijin aure ta janyo muhawara mai zafi a manhajar Twitter, bayan ta bayyana irin namijin da ta ke son aure.

A cikin wani rubutu da ta aikewa shafin @Halal_Match, budurwar ta bayyana cewa tana son samun namiji wanda aƙalla ya ke samun N3m a kowane wata.

Wata budurwa ta bayyana irin mijin da ta ke son samu
Budurwar ta bayyana irin mijin da ta ke so Hoto: @Halal_Match
Asali: Twitter

Ta kuma bayyana cewa tana aiki ne a matsayin injiniyan manhajar na'ura mai kwakwalwa, inda taɓke samun N3.7m a kowane wata.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Da Ta Durfafi Coci Da Nufin Samo Miji Ko Ta Wane Irin Hali

Ta cika buri da yawa

Budurwar ta kuma ƙara da cewa ita ba mai son abin duniya ba ce, amma tana son namiji wanda zai iya ɗauke dukkanin buƙatunta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, wannan rubutun na ta ya tunzura ƴan soshiyal midiya sosai, waɗanda suka caccaketa kan cewa ta cika buri kuma abubuwa da ta ke nema na da wuyar samu.

Wasu sun nunar da ita cewa tana dakushe kanta wajen samun masoyi kan yadda ta mayar da hankali kan kuɗi ba halayya ba.

Wasu sun nuna shakku akan gaskuyarta, inda su ke tunanin da ƙyar idan ta bayyana gaskiya kan abinda ta ke samu da aikin da ta ke yi.

Ga kaɗan daga ciki:

@s_so_true ya rubuta:

"Dey play! Ku kyaleta ta nemi mijin aure a ƙasashen Larabawa masu arziƙin man fetur. Maza da ke a nan fama su ke da mafi ƙarancin albashi na N30."

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Sha Suka Bayan Ta Boye Fuskar Mijinta a Hotunan Shakatawa Da Suka Fita

@barkindo_auwal ya rubuta:

"Ki daina wasa"

@KamorudeenAfee8 ya rubuta:

"Duk wanda ya ke waɗannan abubuwan da kike nema ba zai taɓa kallonki a matsayin zaɓinsa ba, saboda ba ki yi alƙawarin za ki yi biyayya ba a CV ɗin ki. Zai nemi wacce ba ta kai ki ba wacce ya san za ta yi biyayya. Kina samun $5k a wata sannan kina neman mai samun $4k a wata, ko dai bawa kike nema ne"

Kyakkyawar Bahaushiya Ta Zama Soja a Amurka

A wani labarin na daban kuma, wata kyakkyawar Bahaushiya ƴar Najeriya ta ciri tuta inda ta zama soja a ƙasar Amurka.

Kyakkyawar sojan ta bayyana cewa horon da suka samu yana da matuƙar tsanani da wahala. Bidiyonta ya zama abin magana sosai.

Asali: Legit.ng

Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel