Jirgin Kasa Ya Murkushe Sojan Najeriya a Kan Babur a Legas

Jirgin Kasa Ya Murkushe Sojan Najeriya a Kan Babur a Legas

  • Jirgin ƙasa ya kaɗe sojan Najeriya yayin da zai tsallake layin dogo a yankin PWD da ke Ikeja, a jihar Legas
  • Rahoto ya nuna cewa Sojan ya gamu da ajalinsa ranar Laraba da yamma a kokarin tsallake titin jirgin gabannin ya ƙariso
  • Wata majiya a hukumar soji ta tabbatar da cewa an ɗauke gawar mamacin zuwa Asibitin Yaba, jihar Legas

Lagos - Wani Sojan Najeriya ya rasa rayuwarsa ranar Laraba yayin da wani Jirgin ƙasa mai ɗaukar matafiya ya kaɗe shi a yankin PWD da ke Ikeja, jihar Legas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jirgin ƙasan ya baro Ibadan, a hanyar zuwa Iddo a Legas, sa'ilin da ya kaɗe Sojan mai muƙamin Sajan garin tsallake layin dogo a kan Babur.

Sojan Najeriya.
Jirgin Kasa Ya Murkushe Sojan Najeriya a Kan Babur a Legas Hoto: NIgeria Army
Asali: Facebook

Wani ganau ya bayyana cewa haɗarin ya auku da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Laraba, 7 ga watan Yuni, 2023.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: 'Yan Bindiga Sun Halaka Fitaccen Malami a Babban Birnin Jihar PDP

Gabannin mutuwarsa, Marigayi Sojan wanda aka bayyana sunansa da Sajan Jidean Samson, yana aiki ne a rundunar Birged ta 9 da ke sansani a Ikeja, jihar Legas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

Wani Soja ya ce lamarin ya faru a daidai wurin tsallaka layin dogo da ke yankin PWD kuma tuni aka sanar da Birged ta 9 da labarin kaɗe Sojan wanda ya mutu nan take.

Sojan, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda ba shi da hurumin magana a hukumance, ya ce tuni mahukunta rundunar soji suka aika aka ɗauko gawarsa aka kai ɗakin gawa da ke Asibitin Yaba a Legas.

Mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar sashi na 81 a hukumar sojin Najeriya mai kula da jihohin Legas da Ogun, Laftanar Kanal Olabisi Olalekan Ayeni, bai ɗaga kiran tarho da aka masa ba don jin ta bakin hukumar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Wannan na zuwa ne watanni uku bayan wani jirgin ƙasa ya kaɗe motar Bas mai jigilar ma'aikatan gwamnatin jihar Legas da iyalansu a daidai wurin da Sojan ya gamu da ajalinsa.

A wancan lokaci, mutum 6 suka ce ga garinku nan yayin da wasu kusan 80 suka ji raunuka sanadin haɗarin wanda ya auku da safiyar ranar 9 ga watan Maris, 2023.

'Yan Bindiga Sun Halaka Malamin Coci a Babban Birnin Jihar Edo

A wani labarin na daban Wani Malamin coci a jihar Edo ya gamu da ajalinsa a hanyar dawowa daga wurin aikin da aka tura shi.

Rahoto ya nuna cewa 'yan bindiga ne sun harbe Malamin cocin har lahira ranar Laraba, 7 ga watan Yuni, 2023 a kan Titin Agbor, yankin Ikhueniro a cikin birnin Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel