'Yan Bindiga Sun Halaka Malamin Coci a Babban Birnin Jihar Edo

'Yan Bindiga Sun Halaka Malamin Coci a Babban Birnin Jihar Edo

  • Yan bindiga sun halaka wani Fadan Coci a babban birnin jihar Edo yayin da yake hanyar dawowa daga wurin aiki
  • Wata majiya daga Cocin da mamacin ke aiki ta tabbatar da faruwar lamarin da cewa maharan sun yi ajalinsa shi kaɗai
  • A wata sanarwa da Cocin ta fitar, ta ce tuni aka kai rahoton abinda ya faru ga hukumar 'yan sanda don ɗaukar mataki

Edo - Wani malamin cocin Benin Archdiocese, Rabaran Charles Igechi, ya rasa rayuwarsa a hannun 'yan bindiga a Benin City, babban birnin jihar Edo.

Daily Trust ta tattaro cewa 'yan bindiga sun harbe Malamin cocin har lahira ranar Laraba, 7 ga watan Yuni, 2023 a kan Titin Agbor, yankin Ikhueniro a cikin birnin Benin.

Harin yan bindiga.
'Yan Bindiga Sun Halaka Malamin Coci a Babban Birnin Jihar Edo Hoto: punchng
Asali: UGC

Wani Rabaran da ke aiki a Cocin Benin Archdiocese, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda ba shi da hurumin magana kan batun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Jaridar Punch ta rahoton shi yana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Eh dagaske ne an kashe shi, babu wanda ke tare da shi lokacin da 'yan bindigan suka yi ajalinsa."

Ya ƙara da cewa sun tsinci gawar Malamin cocin a kan titin Benin Agbor, inda 'yan ta'addan suka wurgad da shi bayan sun aikata ɗanyen aikin.

Amma shugaban majami'ar Benin Archdiocese, ya ce tuni suka kai rahoton abinda ya faru ga hukumar 'yan sanda domin ɗaukar mataki na gaba.

Bayan haka ya bayyana fatan cewa za'a yi wa marigayi malamin adalci a kan waɗanda suka aikata wannan babban ta'adi.

A wata sanarwar jaje da ya fitar ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, 2023, Akubeze, ya ce Mamacin wanda ya samu kariɓ girma zuwa Fada a watan Agusta, 2022, maharan sun bindige shi a wuya.

Wani sashin sanarwan ya ce:

Kara karanta wannan

Wasu Mahara Sun Harbe Fitaccen Farfesa a Jami'ar Najeriya Har Lahira, Sun Aikata Wani Abu Daban

"Cikin baƙin ciki da ƙunci muna sanar muku da mutuwar ɗaya daga cikin malaman cocinmu, Rabaran Charles Onomhoale Igechi, wanda ya kai wannan matsayi a ranar 13 ga watan Agusta, 2022."
"Har zuwa numfashinsa na karshe, mamacin ya kasance shugaban cocin St. Michael College, Ikhueniro. Mun samun labarin cewa an kashe shi a hanyar dawowa daga wurin aiki ranar 7 ga watan Yuni."

Gwamna Aliyu Ya Tallafawa Mutanen da Harin Yan Bindiga Ya Shafa a Sakkwato

A wani labarin na daban kuma Gwamna Ahmad Aliyu, na jihar Sakkwato ya ki ziyarar jaje garuruwan da kazamin harin yan bindiga ya taɓa kwanan nan.

Gwamna Ahamad Aliyu ya tallafawa iyalan da harin ya shafa da kuɗaɗe da kuma kayan abinci domin rage musu kuncin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel