NAHCON Ta Sanya Wa Alhazan Najeriya Sabuwar Doka Kan Zaman Da Suke a Madina, Ta Ba Da Dalili

NAHCON Ta Sanya Wa Alhazan Najeriya Sabuwar Doka Kan Zaman Da Suke a Madina, Ta Ba Da Dalili

  • Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), ta sanyawa Alhazan Najeriya wata sabuwar doka dangane da kwanakin da za su riƙa yi a Madina
  • Dokar za ta buƙaci duk Alhazan Najeriya su riƙa barin Madina bayan kwanaki biyar da isarsu zuwa birnin Makkah
  • Mataimakin daraktan Hukumar Alhazan, Mousa Ubandawaki ne ya bayar da sanarwar, inda ya ce an ɗauki matakin ne don gujewa takunkumi daga mahukuntan Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), ta sanar da wani tsari da za a buƙaci Alhazan Najeriya da ke Madina da su tafi zuwa Makkah bayan kwanaki biyar da isarsu birnin domin gudanar da aikin hajji.

Mataimakin daraktan yaɗa labarai na hukumar ta NAHCON, Mousa Ubandawaki, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce dokar dai za ta fara aiki ne daga ranar Laraba da ta gabata.

Kara karanta wannan

Ziyara Zuwa Kano: Shigar Da Jarumar Fim Nancy Isime Ta Yi Ya Bada Mamaki, Ana Ta Tafka Mahawara

Matakin dai na zuwa ne biyo bayan korafe-korafen cunkoson Alhazan Najeriya da ake samu a birnin na Madina daga mahukuntan Saudiyya.

An kayyade yawan kwanakin da Alhazan Najeriya za su rika yi a Madina
Hukumar Alhazai ta kayyade yawan kwanakin da Alhazan Najeriya za su rika yi a Madina. Hoto: PM News Nigeria
Asali: UGC

Ubandawaki ya bayyana cewa, a baya hukumar na bai wa Alhazan Najeriya damar zuwa Madina dari bisa dari a matakin farko ko kuma kafin hawan Arafat, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ɗauki matakin ne don kaucewa takunkumi

Sai dai Ubandawaki ya ce an ɗauki wannan matakin ne don kaucewa takunkumin da akan iya sanyawa Najeriya, idan aka ci gaba da samun cunkoso a Madina.

Ya ƙara da cewa sai da aka yi doguwar tattaunawa da kuma yin nazari kafin yanke hukuncin, musamman ma duba da yadda Alhazan Najeriya suka saba zama a Markaz na tsawon lokaci.

Ya bayyana cewa manufar wannan mataki shi ne, don a kaucewa hukunci da ka iya biyo baya kan kawo mahajjata da yawa zuwa Madina fiye da yawan masaukin da za a iya basu, Hajj Reporters ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau

Ya ce daga cikin hukuncin, za a iya tilasta musu ɗaukar Alhazan zuwa wani wajen na daban da bai kai matsayin Markaz ɗin ba.

An ɗauki matakin ne domin amfanin alhazan Najeriya

Ya kuma ƙara da cewa matakin ya zama dole ne domin amfanin Alhazan Najeriya da kuma hukumar ta Alhazan.

Sannan matakin zai taimaka wajen bai wa wasu Alhazan da za su zo daga baya damar zuwa Madina domin suma su yi ziyarar.

Ya yi kira ga jama'a da su fahimci jami’an Hukumar Alhazan da sauran masu ruwa da tsaki gami da basu goyon baya domin samun nasarar aiwatar da wannan sabon tsari.

An gurfanar da matashi a kotu saboda sata a masallaci

A wani labarin na daban, an gurfanar da wani matashi a gaban kotun shari'ar Muslunci bisa laifin satar lasifika a masallaci a Kano.

Sai dai matashin mai suna Halifa Sani, wanda ɗan unguwar Gadon Ƙaya ne, ya musanta tuhumar da ake yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel