“Alkhairi Danko Ne”: Matashi Ya Yi Wa Yar Budurwa Kyautar Piya Wata a Bidiyo, Ta Yi Gwangwaje Shi

“Alkhairi Danko Ne”: Matashi Ya Yi Wa Yar Budurwa Kyautar Piya Wata a Bidiyo, Ta Yi Gwangwaje Shi

  • Bidiyon ban dariya na wata budurwa da ta nemi saurayi mai sana'ar piya wata ya bata kyautar ruwa saboda tana jin kishirwa ya yadu a TikTok
  • A bidiyon, matashiyar ta fada ma matashin mai sana'ar ruwa a titi cewa tana bukatar ya bata kyautar ruwa daya ta sha sai kuwa ya mika mata
  • Jim kadan bayan nan, sai ta fada masa cewa wasa take yi sannan ta ba shi katan-katan na ruwa da lemuka a matsayin kyauta don ya kara jari a sana'arsa

Wani bidiyo mai ban dariya na wata matashiya da ta yi karyan cewa tana jin kishirwa tare da rokon wani mai siyar da piya wata ya bata daya kyauta domin ta kashe kishirwanta ya yadu a TikTok.

A bidiyon, matar ta tunkari matashin wanda ke siyar da ruwa a titi sannan ta roke shi cewa ya taimaka ya bata ruwa daya ta sha.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

Matashi mai piya wata da wata matashiyar budurwa
“Alkhairi Danko Ne”: Matashi Ya Yi Wa Yar Budurwa Kyautar Piya Wata a Bidiyo, Ta Yi Gwangwaje Shi Hoto: @john_nnelena
Asali: TikTok

Mai piya wata ya taimakawa yar budurwa

Matashi mai tsananin kirki ya tausaya sannan ya mika mata daya ba tare da bata lokaci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana haka, sai ta sanar da mutumin cewa duk zolaya ce sannan ta yi masa kyautar lemuka da ruwan roba domin ya kara jari a sana'arsa.

Ta ce yana iya siyar da su sannan ya kara samun kudin kula da kansa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@AdamuNamun ya yi martani:

"Dama Hausawa akwai su da kirki sosai."

@AbasikponkeEkpenyon ta ce:

"Mutanen kirki...Ina son Hausawa da jinina..sun fi kowa kirki."

@Shantel ta rubuta:

"Allah ya albakace ki yar'uwata."

@user1254852623948 ya yi martani:

"Wannan wani aiki ne mai kyau."

@Raffiabaskets.comkag ta yi martani:

"Bari na bibiye ki saboda soyayyar da kika nuna mana."

@E4mah:

"Dama Hausawa akwai kirki."

@shamie:

Kara karanta wannan

An Samu Matsala: Dan Najeriya Ya Shiga Tashin Hankali Bayan Ya Gano Kullum Da Tsakar Dare Motarsa Tana Kunna Kanta

"Allah ya yi maki albarka hajiya."

"Akwai irinmu sosai": Kyakkyawar budurwa inyamura ta ce ita Musulma ce kuma tana alfahari da haka

A wani labari na daban, wata matashiya ta bayyana cewa ita yar kabilar Igbo ce kuma Musulma tun daga haihuwarta.

Matashiyar ta ce tana fuskantar kalubale sosai wajen tabbatarwa mutane cewa akwai irinsu a doron kasa kuma suna tsananin alfahari da kasancewarsu Musulmai yan Igbo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel