“Sharrin Mutanen Boye Ne”: Matashi Ya Gano Cewa Motarsa Na Kunna Kanta Duk Dare

“Sharrin Mutanen Boye Ne”: Matashi Ya Gano Cewa Motarsa Na Kunna Kanta Duk Dare

  • Wani dan Najeriya ya ce ya siya wata mota kirar Venza wacce ke kunna kanta duk tsakar dare
  • Fidelis Ozuawala ya aika labarinsa mai ban al'ajabi ga Legit.ng sannan ya ce ya gaji a lokacin da matsalar ta fara
  • Ya ce cike da kosawa, ya dauki motar zuwa wajen fasto dinsa don addu'o'i sannan ya kai shi ga wani boka don neman mafita

Wani dan Najeriya wanda ya siya sabuwar mota kirar Venza ya kosa saboda motar na tayar da kanta da kanta.

A wani labari da ya aikewa Legit.ng, Fidelis Ozuawala, ya ce sabuwar motar tasa kirar Venza na tayar da kanta duk tsakar dare.

Matashi tsaye a gaban mota
“Sharrin Mutanen Boye Ne”: Matashi Ya Gano Cewa Motarsa Na Kunna Kanta Duk Dare Hoto: Fidelist Ozuawala
Asali: Facebook

Fidelis ya shiga rudani sannan ya kosa da lamarin saboda shi da iyalinsa za su kwanta bacci sannan sai motar ta fara tururi."

Kara karanta wannan

“Na Fada Maku Ni Mace Ce”: Budurwa Ta Saki Bidiyo Don Tabbatar Da Jinsinta, Mutane Sun Magantu

Mutane da dama, ciki harda danginsa sun ce motar na karkashin kulawar mutanen boye, kuma matarsa ta shawarce shi da ya gaggauta siyar da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fidelis ya kai motarsa wajen boka da fasto

Sai dai kuma, Fidelis ya ki maimakon haka sai ya fara neman mafita ga matsalar. Ya dauki motar zuwa wajen fasto dinsa, wanda ya yi addu'o'i a kai, amma lamarin bai daina ba.

Ya kai motar wajen boka wanda shima ya yi mata wankan magunguna sa surkulle, amma matsalar ta ci gaba.

Ya yanke shawarar neman wata mafita bayan ya gaza samun mafita daga masu magani. Sai ya yi bincike a intanet.

Ya ce:

"A wannan karon, na yanke shawarar bincike a intanet. Na bincika Google sannan daga nan na garzaya YouTube, a nan ne naga motoci da dama da mutane da dama da ke fuskantar irin matsalar.

Kara karanta wannan

“Bayan Shekaru 15 Da Aure”: Matar Aure Ta Koka a Bidiyo Yayin da Mijinta Ya Fada Mata Ita Ba Ajinsa Bace

"Matsalar mai sauki ce, wasu motocin waje daga wurare masu sanyi suna saka wata na'ura da ke sanya injin ya fara aiki idan zafinsa ya sauka sosai don kada injin ya yi kasa, yana dumama injin sannan ya hana shi toshe sassa masu muhimmanci.
"Wani bincike, bincike mai sauki ya kore shakku na, kuma da na cire na'urar sai motar ta daina tashi da kanta gaba daya."

Fidelis ya fada ma Legit.ng cewa koda dai baya amfani da motar yanzu, tana nan ya ajiye ta.

Jama'a sun yi martani

Golden-Ubachukwu Asteroid ya ce:

"Wannan rubutu ne mai ban sha'awa da jan hankali yallabai. Gakiya ne, Amsar matsalolinmu na iya kasancewa a bincike mai sauki."

Ephraim Nick Edeh ya ce:

"Lallai ka sha gwagwarmaya sosai fa...Allah ne karfinka kuma shi zai kare ka."

Bafulatana ta haddasa cece-kuce bayan ta bayyana irin mijin da take so ta aura

Kara karanta wannan

Kujerar Dan Majalisar Tarayyar Nasarawa: Al Makura Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Ya Janye Karar Da Ya Shigar Kotun Zabe

A wani labari na daban, wata kyakkyawar Bafulatana ta ɗauki hankula sosai a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa tana matuƙar son maza Inyamurai.

Kyakkyawar budurwar wacce Musulma ce sannan ƴar asalin jihar Kano, ta bayyana cewa tana fatan ta auri miji Inyamuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel