“Na Ga Rayuwa”: Musulma Yar Igbo Ta Magantu, Ta Ce Tana Matukar Alfahari

“Na Ga Rayuwa”: Musulma Yar Igbo Ta Magantu, Ta Ce Tana Matukar Alfahari

  • Wata matashiya yar Igbo wacce ta kasance Musulma ta bayyana addininta cike da alfahari a soshiyal midiya, tana mai cewa a haka aka haifeta
  • Da take karin haske game da tushenta, matashiyar yar Igbon ta ce tana shan wahala wajen yi wa mutane bayani
  • Rubutunta ya yadu yayin da Musulmai da dama da wadanda suke yan Igbo suka nuna mata goyon baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya yar Najeriya ta bayyana cewa ita yar kabilar Igbo ce kuma Musulma tun daga haihuwarta.

A cewar matashiyar, gaba daya iyayenta yan kabilar Igbo ne kuma Musulmai tun daga tushe sannan tana mamaki cewa yaran da za ta haifa a gaba suna da jan aiki na yi wa mutane bayanin kabila da addinin mahaifiyarsu.

Ba kasafai dai aka cika samum musulmi ba daga kudu maso gabashin Najeriya inda kabilar Ibo suka fi yawa a kasar.

Kara karanta wannan

“Bai Taba Cin Amanata Ba”: Budurwa Ta Ki Amsa Tayin Saurayin Da Suka Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya, Ta Fadi Dalili

Shi yasa idan hakan ya faru sai ya zama tamkar abin mamaki ga wasu mutane.

Matashiya da mijinta
“Na Ga Rayuwa”: Musulma Yar Igbo Ta Magantu, Ta Ce Tana Matukar Alfahari Hoto: @mahasha_photography
Asali: TikTok

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata wallafa da ta yi a TikTok, ta ayyana addininta cike da alfahari yayin da take baje kolin sahibinta. Ta ce yana da matukar wahala gareta yin bayanin addini da kabilarta.

"Yaran da zan haifa a gaba suna da jan aiki yin bayani cewa mahaifiyarsu Igbo ce kuma Musulma tun daga haihuwa, saboda na ga rayuwa yi wa mutane bayanin cewa iyayena dukka Igbo ne kuma Musulmai tun daga haihuwa."

A wata wallafar, ta bayyana cewa akwai Musulman Igbo kuma suna alfahari da addini da kabilarsu.

"Ku yarda da ni ko kada ku yarda mu Musulmai Igbo akwai mu kuma kwarai muna alfahari da addini da kabilarmu Alhamdulillah."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

MELODYSWEET1986 ta ce:

Kara karanta wannan

“Namiji Baya Kadan”: Wata Mata Yar Najeriya Ta Baje Kolin Saurayinta Mai Karancin Shekaru

"Ni daga jihar Abia kuma na auri Musulmi."

ibrahimsaniib ya ce:

"Masha Allah, Allah ya dauki ranki a matsayin Musulma sannan ya ba ki Aljannatul Firdausi ameen summa ameen."

user6775657544743 ya ce:

"Ina taya ki murna kuma a ra'ayina ina son auren yar Igbo da take Musulma saboda ina son addinin sosai."

Bekky ta ce:

"Na yi bayani har na gaji yar'uwata wasu ma basa yarda da ni har sai na fada masu wurare a kauyena."

Budurwa ta koka kan masu kiranta da namiji, ta bayyana jinsinta a bidiyo

A wani labarin kuma, wata matashiya ta magantu a kan yadda wasu ke yi mata kallon namiji a soshiyal midiya.

Ta tabbatar masu da cewar ita din mace ke don bata dauke da kowani sassa irin na da namiji a jikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel