“Abun Akwai Ciwo Sosai”: Matashiya Ta Ki Amsa Tayin Saurayin Da Suka Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya

“Abun Akwai Ciwo Sosai”: Matashiya Ta Ki Amsa Tayin Saurayin Da Suka Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya

  • Wata matashiya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta fadi dalilinta na kin amsa tayin auren masoyinta
  • Duk da cewar sun shafe tsawon shekaru takwas suna soyayya, budurwar ta ki amsa bukatarsa na son aurenta
  • Da take bayyana dalilinta na yin haka, ta ce yana so ya koma makaranta kuma ba zai samu isasshen kudin kulawa da ita ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiyar budurwa ta bayyana dalilinta na kin amsa tayin auren saurayinta bayan sun shafe tsawon shekaru takwas suna shan soyayya.

A cewarta, tana ganin ba abun da ya dace ya yi bane a yanzu saboda bai da wani kwakkwaran tushen samun kudi yanzu.

Budurwa ta ki amsa tayin auren saurayinta
“Abun Akwai Ciwo Sosai”: Matashiya Ta Ki Amsa Tayin Saurayin Da Suka Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya Hoto: Vladimir Vladimirov, Dean Mitchell/ Getty Images.
Asali: Getty Images

Ta bayyana cewa zai tafi jami'a inda zai shafe tsawon shekaru biyar zuwa shida yana karatu.

Sun haifi da daya tare kuma ta damu da jin dadin yaron idan suka yi aure yanzu sannan suka sake haifar karin 'ya'ya ba tare da wani kwakkwaran hanyan samun kudi ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yarinya Yar Shekaru 4 Da Ta Iya Kitso Ya Girgiza Intanet, Sun Tofa Albarkacin Bakunansu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalamanta:

"Na yi soyayya da uban dana na tsawon shekaru 8. Soyayya mafi kyau a rayuwata. BAI TABA cin amana ba. Ya nemi aurena a farkon shekarar nan. Na ki amsa tayinsa. Gayen ya ci gaba da rasyuwa. Abun akwai ciwo, akwai ciwo sosai. Ban fada masa dalilaina ba kuma na yi tunanin Kanti ya fahimta.
"Dalili: Shine bangon jinginar yan'uwa. Har yanzu yana kokarin kammala gidansa, zai tafi jami'a a shekara mai zuwa na shekaru 5-6, ba za a samu kudin shiga ba a shekara mai zuwa, na bukace shi da ya tsaya har sai na fara aiki. Watan danmu 5 yanzu. Shi nake tunani kawai. Yadda nake kallon abubuwa kenan.
"Magana ake ta lafiyar kwalwalwarsa. Ta yaya za ka yi fama da jami'a, yaro, mata da dangi? Kuma rayuwar jami'a akwai tsada. Ba zan jefa shi a wannan hali ba. Idan da ya ce "na samu wannan" sannan ya yi bayanin yadda ba zan ki amsa tayinsa ba."

Kara karanta wannan

Zololo kenan: Mata mai tsawon da ya kusan taba 'ceiling' ta dauki hankalin jama'a

Jama'a sun yi martani

Dima Phoshoko ta ce:

"Na fahimce ki. Yanzu fada mani, kin ki amsa tayin auren amma kina son ci gaba da soyayyar? Menene zai dunga yi a aure da baya yi yanzu a matsayin sauray? Ina ganin an riga an gina wasu soyayyar kamar aure dama."

Demba ya ce:

"Bai yi kuskure ko daidai ba amma ba zan ga laifinsa don ya ci gaba da harkokinsa ba. A kodayaushe maza ake kira masu bata lokaci a soyayya idan ba a yi aure ba."

Kalli wallafar a kasa:

Budurwa ta nunawa duniya saurayinta da ta girma nesa ba kusa ba

A wani labarin kuma, wata yar Najeriya mai dan shekaru ta haddasa cece-kuce bayan ta baje kolin matashin saurayinta a soshiyal midiya.

Da take yada wani bidiyo dauke da hotunanta da na yaron, matashiyar ta ce bata damu da tazarar shekarun da ke tsakaninsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel