Da Dumi-Dumi: Ma'aikatan Shari'a Na Kasa Sun Shiga Yajin Aiki

Da Dumi-Dumi: Ma'aikatan Shari'a Na Kasa Sun Shiga Yajin Aiki

  • Ƙungiyar ma'aikatan sharia ta ƙasa (JUSUN) ta sanar da shiga yajin aikin gama-gari daga ranar Laraba, 7 ga watan Yuni
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta tsunduma yajin aikin ne saboda cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi
  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ita ma na shirin shiga yajin aiki duk da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na hana aukuwar hakan

Abuja - Ƙungiyar ma'aikatan shari'a ta ƙasa (JUSUN), ta sanar da shiga yajin aiki bisa cire tallafin man fetur, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

A cikin wata sanarwa, babban sakataren ƙungiyar na ƙasa, M.J. Akwashiki, ya umarci dukkan rassan ƙungiyar da su fara shirin daina ayyukansu daga ranar Laraba, 7 ga watan Yunin 2023.

Kungiyar ma'aikatan shari'a ta shiga yajin aiki kan tallafin man fetur
Cire tallafin man fetur ya janyo wahala a Najeriya Hoto: Leadershiphausa.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan hukuncin da ɓangaren zartarwa na ƙungiyar ta ƙwadago ta ƙasa (NLC), ya cimmawa kan tashin gwauron zaɓi da farashin man fetur ya yi.

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan hukuncin na zuwa ne biyo bayan matsayar da ɓangaren zartarwa na ƙasa na ƙungiyar ƙwadago (NLC) ya cimmawa a zamansu na ranar 2 ga watan Yunin 2023, kan ƙarin da farashin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ta hannun kamfanin NNPCL."
“Dukkanin mataimakan shugaban ƙungiyar na shiyya-shiyya su sanar da shugabannin rassan ƙungiyar, su tabbatar sun tattaro mambobinsu domin bin wannan umarnin."

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa za ta za ta shiga yajin aiki

Kamfanin man fetur na ƙasa Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL), ya ƙara kuɗin man fetur da sama da kaso 200%, wanda ya sanya farashin lita ɗaya ya koma N488 da N557, rahoton The Nation ya tabbatar.

Hakan ya sanya ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta sanar da tsunduma cikin yajin aiki daga ranar Laraba, 7 ga watan Yunin 2023.

Gwamnatin tarayya ta zauna da ƙungiyoyin ƙwadago a satin da ya gabata kan barazanar da suka yi na shiga yajin aiki.

Gwamnatin Tinubu Na Shirin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur

A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Tsohon gwamnan ya ce shugaban ƙasar na shirin inganta albashin ma'aikata da rarar kuɗin cire tallafin man fetur ɗin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel